Bidiyon kyakyawar budurwa sanye da hijab ta na kwallon kwando, har ta na yanke maza

Bidiyon kyakyawar budurwa sanye da hijab ta na kwallon kwando, har ta na yanke maza

  • Wata kyakyawar budurwa mai suna Jamad Finn ta na amfani da kwallon kwando wurin sauya tunanin mutane a kan 'yan mata musulmai
  • A wani bidiyon tattaunawa da aka yi da Jamad, ta ce sau da yawa mutane kan yi mamakin ganin yadda ta ke wasan sanye da hijab
  • Babu shakka bidiyon hirar ta janyo maganganu tare da tsokaci da yawa daga jama'ar da suka kalla, ganin cewa musulmar budurwa ce

Wata matashiyar kyakyawar budurwa maisuna Jamad Finn, ta kafa tarihi a kwallon kwando. Wallafar ta a kafar sada zumuntar ta janyo maganganun mutane daban-daban ganin yadda ta yi suna a wasan.

A wata tattaunawa da tayi da BBC, budurwar ta ce a bayyane yake cewa jama'a basu taba ganin budurwar musulma ta na kwallon raga ba kuma sanye da cikakkun kayan Musulmi.

Read also

Tirkashi: Uwa ta kashe 'ya'yanta biyar saboda kishi, ta hadu da fushin alkali

Bidiyon kyakyawar budurwa sanye da hijab ta na kwallon kwando, har ta na yanke maza
Bidiyon kyakyawar budurwa sanye da hijab ta na kwallon kwando, har ta na yanke maza. Hoto daga @_jamaad
Source: Instagram

Ina bukatar uzirin yin wasa

Ta ce akwai yuwuwar sanin ta da aka yi ya zama dalilin da ta yi suna a yanar gizo. Daya daga cikin bidiyon ta ta na yanke maza ya nuna yadda ta kware a wasan. Yadda ta ke canza hannun rike kwallon kadai zai nuna gwanancewarta.

Finn ta ce a yayin da ta ke girma, ta kan samu uzirin da zai sa ta yi kwallon balle a gaban iyayenta yadda za su bar ta tayi wasan ta.

Abubuwa masu tarin yawa sun sauya

Ta kara da cewa, yanzu da ta yi suna a kan abinda ta ke yi da kwallon kwando, wasu za su iya amfani da irin shuhurar ta wurin bai wa iyayensu uzirin son yin wasan kwallon kwando.

Read also

Bayan lafawar tawagar Gana a Benue, wasu muggan makasa sun fito da sabon salon kisa

Finn ta ce ta so hakan yayin da ta ke girma. Budurwar ta ce:

"Mutane masu tarin yawa a yanzu idan sun ga mace musulma ta na wasannin motsa jiki ba su yin mamaki.
"A yanzu an san cewa ba kullum muke zaune a gida ba kuma tunanin jama'a game da takunkumin da ake saka mana ba haka bane."

A yanzu ni zan dinga koyawa wasu wasan

A yayin da yara mata suka fara nuna sha'awar koyon wasan da ta ke yi, budurwar ta yanke shawarar kafa sansanin kwallon raga tare da koya musu.

Ta fara hakan ne tun ta na kwaleji. Mai wasan kwallon ragar ta ce wasan ya sauya rayuwar ta duk da ita mace ce mai kunya.

Hotunan jami'o'i 4 na farko a duniya duk a Afrika suke, mace ta kafa 1 daga ciki

A wani labari na daban, jama'a masu yawa sun yi zaton tsofaffin jami'o'i na duniya za su kasance a Turai. Amma kuma ba hakan ba ne, Afrika ita ce nahiyar da aka fara samun jami'o'i hudu masu dadewa kuma daya daga cikinsu mace ce ta samar da ita.

Read also

Funmilayo Ransome-Kuti: Abubuwa 4 game da macen da ta fara tuka mota a Najeriya

Legit.ng ta gabatar muku da tsoffin jami'o'in duniya kamar yadda Erudera ta bayyana.

Source: Legit.ng

Online view pixel