Gwamnan Kaduna El-Rufai ya tsokano mutanen Kano, yace Kanawa bayin Zazzagawa ne

Gwamnan Kaduna El-Rufai ya tsokano mutanen Kano, yace Kanawa bayin Zazzagawa ne

  • Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi karin haske a kan alakarsa da Khalifa Muhammadu Sanusi II.
  • Nasir El-Rufai ya tabo wannan magana ne da yake bayani a kan sauya-sauyen da ya yi a gwamnatinsa.
  • Wasu na tunanin kalaman Sanusi II suka jawo Dattijo ya rasa mukaminsa, ya koma tsohuwar kujerarsa.

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya tsokani mutanen Kano, yayin da yake bayanin alakar da ke tsakaninsa da Muhammadu Sanusi II.

Jaridar Daily Trust ta ce Malam Nasir El-Rufai ya jawo fadan Kanawa ne a lokacin da yake karin haske a kan abin da ya sa ya canza wasu kwamishinoninsa.

Kamar yadda kuka ji a baya, gwamnan ya yi fatali da rade-radin da ake yi na cewa ya sauke Muhammed Sani Abdullahi saboda Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya magantu kan rade-radin tasirin tsohon sarki Sanusi a tafiyar da gwamnatinsa

Mai girma Gwamnan yace babu abin da ya hada matakin da ya dauka da wasan da aka yi tsakanin Sanusi II da hadiminsa wajen taron jawo hannun jari.

Da aka yi hira da Malam El-Rufai a game da wannan rade-radi, sai yace ba kalaman tsohon Sarkin na Kano suka sa ya canza shugaban ma’aikatan fadarsa ba.

Gwamnan yace cire Mohammed Sani Abdullahi daga mukaminsa ya taimaka masa domin wasu suna tunanin da gangan aka shigo da shi cikin gidan gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Kaduna El-Rufai
Gwamnan Kaduna, El Rufai da Sanusi II Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kanawa bayin zazzagawa ne

“Wasan da aka yi tsakaninsa (Mohammed Sani Abdullahi) da Khalifa Muhammadu Sanusi, wasa ne mai tarihi tsakanin Zaria da Kano.”
“Kamar yadda kuka sani, mutanen Kaduna suna ganin wadanda suka fito daga Kano a matsayin bayinsu.” – Gwamna Nasir El-Rufai.

El-Rufai yace masu alakanta sauye-sauyen da aka yi da kalaman Sanusi II, ba su san gwamnati ba, yace duk abin da ya yi, sai wasu sun yi masa wani irin fassara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ban gamsu da ayyukan da Ganduje ya yi a Kano ba, In ji Kwankwaso

“Don haka masu tunanin ba’ar bawa da uban gidansa za ta jawo a cire wani, ba su san irin matsalolin da muke so mu magance a Kaduna ba.”
“Manyan jiha suna kukan ba na jin shawara, to don haka ina mamakin jin cewa abokina yake fada mani abin da zan yi ko in bari.” - El-Rufai

El-Rufai yace kafin ya canza mukamai, sai da ya zauna da hadimin na sa da mataimakiyar gwamna, kuma Dattijo bai nuna bai sha’awar komawa Kwamishina ba.

An yi sauya-sauye a Kaduna

Gwamnatin El-Rufai ta sanar da sauye-sauye a majalisar gudanarwa a ranar 12 ga watan Oktoba a wata sanarwa da mai bada shawara, Muyiwa Adekeye ya fitar.

A cikin sauye-sauyen, gwamnan ya nada sababbin mukamai ga wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnati, ya kuma cire shugaban ma'aikatan fadarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel