Tsohon Sanatan Kaduna yana so a ayyana ‘Yan bindiga a matsayin Ma’aikatan Gwamnati

Tsohon Sanatan Kaduna yana so a ayyana ‘Yan bindiga a matsayin Ma’aikatan Gwamnati

  • Sanata Shehu Sani ya caccaki Gwamnatin APC a kan kin ayyana ‘Yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda
  • Kwamred Sani ya nemi Gwamnatin Tarayya ta sa ‘Yan bindiga a matsayin ma’aikatan gwamnati
  • Tsohon Sanatan ya yi wa masu mulki gatse ne saboda ta ki shawarwarin da jama’a suke ta badawa

Abuja - Tsohon Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya sake magana a kan abubuwan da suka shafi kasa, a wannan karo ya tabo batun rashin tsaro.

Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ma’aikatan gwamnatin tarayya, tun da an gaza sa su a jerin ‘yan ta’adda.

A ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, 2021, Sanata Shehu Sani ya yi amfani da shafin Twitter, yana caccakar matakin da gwamnatin APC mai-ci ta dauka.

Kara karanta wannan

2023: Najeriya za ta daidaita idan 'yan Najeriya suka ba PDP dama, inji gwamna

Sanata Sani ya koka kan yadda miyagun ‘yan bindiga suke hallaka Bayin Allah a wuraren ibadunsu, amma an ki ayyana su a jerin ‘yan ta’adda a Najeriya.

Me Shehu Sani ya fada a Twitter?

“Su (‘yan bindigan) sun kashe musulmai masu ibada a masallatansu a jihohin Neja da Katsina, sun kashe kiristoci a cocinsu a jihar Kaduna.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan gwamnati ba za ta iya ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda ba, ta ayyana su a matsayin ma’aikatan gwamnatin tarayya.” – Sanata Shehu Sani.
Tsohon Sanatan Kaduna
Shehu Sani Hoto: newswirengr.com
Asali: UGC

Babu amfanin rufe hanyoyin sadarwa

Kafin nan tsohon ‘dan majalisar ya fito ya yi tir da harin da aka kai a cocin darikar Baptist a kauyen Kakau Daji, a jihar Kaduna, yace lamarin abin takaici.

Da yake Allah-wadai da harin ‘yan bindigan, Shehu Sani yace toshe layukan wayoyi da hukumomin gwamnati suka yi a wasu jihohi bai yi amfani ba.

Kara karanta wannan

CAN ga FG: Ya kamata a garkame Sheikh Gumi saboda yiyuwar alaka da 'yan bindiga

‘Dan adawar ya yi wannan magana ne jim kadan bayan sun halarci taron zaben shugabannin PDP.

Kungiyar CAN tayi martani

Shugaban kungiyar kiristoci na CAN na jihar Kaduna, Rabaren Joseph Hayab, ya fitar da jawabi bayan wannan hari, yace sha’anin tsaro ya tabarbare a yau.

“Ana kashe al’umma kamar kaji, babu abin da ake yi sai fitar da jawabi da sunan ta’aziyya. Wadannan miyagu sun dade suna yi mana ta’adi.” – Hayab.

Asali: Legit.ng

Online view pixel