Akwai yiwuwar sabon samufurin Coronavirus ya bulla, za ayi tayi wa mutane rigakafi a Legas

Akwai yiwuwar sabon samufurin Coronavirus ya bulla, za ayi tayi wa mutane rigakafi a Legas

  • Babajide Sanwo-Olu yana so ayi wa mutum miliyan 4 rigakafin COVID-19 a Legas
  • Gwamnan ya kaddamar da kamfe domin a yawaita allura domin a yaki Coronavirus
  • Idan aka yi sake, wani sabon na’u’in cutar zai iya bayyana nan da karshen shekara

Lagos - A ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba, 2021, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas yace watakila sabon samfurin COVID-19 ya bayyana.

Daily Trust ta rahoto Gwamna Babajide Sanwo-Olu yana cewa akwai yiwuwar sahu na hudu na cutar ya bullo yayin da ake ta dumfarar bikin kirisemti.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da ake kaddamar da kamfe na musamman da aka shirya domin yi wa mutane har miliyan hudu rigakafi.

Babajide Sanwo-Olu yana so nan da karshen shekara a samu akalla mutane miliyan hudu da sun samu allurar rigakafin wannan cuta ta murar mashako.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci, PFN ta bukaci Gwamnati ta kama Malamin Musulunci, Ahmad Gumi

A cewar Sanwo-Olu, wannan yana cikin dabarun da za su hana cutar ta sake bayyana a jihar Legas.

Gwamnan Legas
Sanwo Olu yana karbar allurar COVID-19 Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

An ci burin yi wa mutane miliyan rigakafi a Legas a 2021

Jaridar Sun tace an kaddamar da wannan kamfe ne a dakin taro na Civic Center, da ke Victoria Island.

An yi wa wannan shiri da aka bullo da shi mai taken: “Operation Count Me in 4 Million Lagosians Vaccinated Against COVID-19” domin a yaki annobar.

Gwamnatin Legas da hadin-gwiwar hukumar NPHCDA ne suke yi wa mutane rigakafin cutar. Ana iya yi wa duk wanda ya haura shekara 18 allurar kariyar.

Gwamnatin jihar tace za ta bude cibiyoyin yin rigakafin cutar ta COVID-19 a wuraren da ake samun cunkoso sosai, domin a takaita yaduwarta a Legas.

Kara karanta wannan

Mutane 200, 000 sun rungumi tsarin E-Naira a cikin awanni 24 da fitowa Najeriya

Hakan zai taimaka wajen bada kariya ga mutanen da ke zaune a wuraren da rigakafin ya yi wuya. Sannan Gwamnan yace za a rika yawo da motocin magani.

Mutum miliyan 3 aka yi wa rigakafi a wata 8

Watanni kusan takwas da suka wuce ne aka ji cewa allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca sun iso kasar nan ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Amma shugaban hukumar HPHCDA, Dr. Shuaib Faisal yace duka-duka mutane miliyan 2.9 aka yi wa rigakafi a Najeriya, saboda mutane ba su kawo kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel