Dalibin Najeriya ya kammala digiri bayan shekaru 13 ana gwagwarmaya a Jami'ar UNIJOS

Dalibin Najeriya ya kammala digiri bayan shekaru 13 ana gwagwarmaya a Jami'ar UNIJOS

  • Allah ya yi Jonathan Ogboffa ya kammala karatu a Jami’ar UNIJOS
  • Mutane sun ce Kwamred Aluta Jango ya yi shekaru 13 a makarantar
  • Wannan Bawan Allah ya yi ta gantali kafin ya samu shaidar Digirin

Plateau - Bayan sama da shekaru goma yana makaranta, wani Bawan Allah mai suna Jonathan Ogboffa ya gama karatun digirinsa a jami’ar UNIJOS.

Legit.ng ta fahimci Jonathan Ogboffa wanda aka fi sani da Aluta Jango ya na cikin tsofaffin fuskokin da aka sani a jami’ar tarayyar da ke garin Jos.

Jonathan Ogboffa ya karanta ilmin koyar da tarihi ne a fitacciyar jami’ar da ke jihar Filato.

UNIJOS Breaking News sun wallafa hoton Aluta Jango a shafinsu na Facebook yana dauke da wata riga da aka rubuta “Most Senior Comrade Jango."

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Rahotannin da Legit.ng ta samu ya bayyana cewa Kwamred Aluta Jango ya shiga harkar siyasar makaranta, wanda hakan ya sa ya dade bai gama karatu ba.

Aluta Jango ya yi ta yawo daga wannan sashe zuwa wannan sashe a shekarun da ya yi a jami’ar ta Jos, kafin ya samu ya karkare digirin sa a shekarar nan.

Jonathan Ogboffa
Jonathan Ogboffa Hoto: UNIJOS Breaking News
Source: UGC

Mutane na taya Aluta Jango murna a Facebook

Mutane da dama sun fito suna taya Jonathan Ogboffa murnar kammala karatu bayan tsawon lokaci. Bisa dukkan alamu tun kimanin shekarar 2008 ko 2009.

“Babban farin ciki ga malaman da suka rike shi a shekaru 13. Akalla yanzu sun samu wani abin yi da rayuwarsu. Tir da Najeriya.” – TarOrFeeek.
“Ina taya murna ga shugaban ‘yan gwagwarmaya. Barka Jango.” - Jeffery David.

Read also

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

Da a ce makarantar nan a inda aka san abin da ya kamata ne, da ya kammala karatu tun tuni, har ya samu aikin yi, yana samun kudi mai tsoka. – ikillbrokehoes.

Shi kuma wani ya ce karatu a Najeriya akwai wahala, shi ya sa ‘ya ‘yana ba za su yi karatu a Najeriya.

A ka’ida ya kamata a ce a cikin shekaru hudu an kammala karatun digiri a ilmin koyar da tarihi.

A wasu jami’o’in da ke Najeriya, idan mutum ya kara shekaru biyu a kwas din da ake kammalawa a shekaru hudu, za a kore shi ne gaba daya daga jami’ar.

Source: Legit.ng

Online view pixel