Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

  • Jami'in dan sanda ya shawarci 'yan Najeriya da su ba da 'yan bindiga hadin kai don neman zaman lafiya
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da wasu 'yan ta'adda da aka kama a sassa daban-daban na kasar
  • Ya ce, ba da hadin kan zai taimaka wajen kubutar da mutanen da aka sace ba tare da an cutar dasu ba

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne Babbar Rundunar ‘Yan Sanda ta shawarci 'yan Najeriya da su ba da hadin kai ga masu garkuwa da mutane idan sun fada hannunsu don kare lafiyar su da kuma gujewa kashe su.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar (FPRO), Frank Mba, wani Kwamishinan 'yan sanda, ya ba da shawarar ne a Abuja yayin gabatar da mutane 48 da ake zargi da aikata manyan laifuka.

Read also

Yadda 'yan sanda suka bindige mai sana'ar walda suka ce jagoran IPOB ne

Wadanda ake zargin har da wani Haliru Mohammed mai shekaru 25 wanda ya shirya garkuwa da 'yar uwarsa, Binta, don ya karbi fansa saboda ya gaza biyanta bashin da ta ke binsa.

Babbar magana: Ku ba 'yan bindiga hadin kai ku zauna lafiya, 'yan sanda ga 'yan Najeriya
Jami'an 'yan sandan Najeriya | Hoto: dailynigerian.com
Source: Depositphotos

CP Mba tare da kwamandan 'yan sanda na rundunar IRT, ya shaida wa manema labarai cewa jami'an' yan sandan IRT karkashin jagorancin DCP Olatunji Disu sun kamo wadanda ake zargin a wurare daban-daban na bayan bin sahihan bayanan sirri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin gabatarwar, Mba ya shawarci jama'a musamman wadanda aka sace da kada su yi gwagwarmaya da 'yan bindiga, kawai su ba da hadin kai domin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro su kawo musu dauki.

Hakazalika, ya bayyana cewa, a kullum jami'an 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro na iya kokarin ganin sun ceto mutanen da aka sace, musamman idan aka samu bayanan sirri.

Read also

Karshen zamani: Mahaifi ya yi hayar 'yan daba su lakadawa malamin 'yarsa duka

Jami'an tsaron Najeria na ci gaba da samun nasara kan 'yan bindiga, inda ake yawan samun rahotannin kamu ko hallaka 'yan ta'addan.

A makon jiya, jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun cafke wani sojan karya, Hayatu Galadima da abokin aikin sa, Hamisu Adamu.

An bayyana cewa mutanen biyu suna kokarin shigar da muggan kwayoyi, alburusai da kayayyakin sadarwa ga 'yan bindiga a Kaduna lokacin da aka cafke su.

Femi Babafemi, daraktan yada labarai na NDLEA, a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook na hukumar a ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a kan babbar hanyar Gwagwalada, Abuja.

An cafke kasurgumin kwamandan 'yan bindigan da ya addabi jihar Zamfara

A bangare guda, Ayuba Elkanah, kwamishinan 'yan sanda a Zamfara, ya ce rundunar 'yan sanda ta cafke wani kasurgumin kwamandan 'yan bindiga mai suna Bello Rugga, The Cable ta ruwaito.

Read also

Zamfara na fama da 'yan gudun hijira 700,000, gidaje 3,000 sun halaka, Matawalle

Elkanah ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake gabatar da wanda ake zargi kwamanda ne tare da wasu mutane 21 da ake zargi da fashi da makami a Gusau.

Ya ce an kashe wasu 'yan bindiga biyar yayin wani samame da suka kai a karamar hukumar Gummi ta jihar.

s

Source: Legit

Online view pixel