Jerin Ƙasashen Afirka 12 da Tarin Basussuka Ya Masu Katutu Kuma Ya Zama Barazana

Jerin Ƙasashen Afirka 12 da Tarin Basussuka Ya Masu Katutu Kuma Ya Zama Barazana

Mafi yawan kasashen nahiyar Afirka na fama da basussuka da suka masu katutu, lamarin da ya zama kalubale ga ci gaban tattalin arzikin waɗannan ƙasashe.

A wannan shafin, Legit Hausa ta tattaro muku ƙasashen da basussuka suka fi yi wa katutu a nahiyar Afirka kamar yadda rahoton asusun bada lamuni (IMF) ya nuna.

Cabo Verde da wasu kasashen da ke fama da bashi.
Kasashen da basussuka suka yi wa katutu a nahiyar Afirka Hoto: Jose Maria Neves, Filipe Nyusi, DRC Today
Asali: Facebook

Rahoton ya yi amfani da yawan bashi da ƙarfin tattalin arziki (GDP), wanda ya kasance ma'auni na kai tsaye da ke nuna basussukan da ake bin ƙasa da karfin arzikinta, an sa ma'aunin a 100%.

Karancin kason na nuna daidaiton tattalin arziki, ma'ana kasar na samun isasshen kudin shiga don biyan basussukan, yayin da kaso mai yawa ke nuna kalubalen da za a iya fuskanta wajen biyan bashin.

A cewar asusun ba da lamuni na duniya (IMF), ƙasashen Afirka mafi cin bashi su ne:

Kara karanta wannan

Masu kantin da ya hana 'yan Najeriya sayayya sun amsa gayyatar hukumar FCCPC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Cabo Verde (109.7%)

Cabo Verde, wata ‘yar ƙasa da ke kan tsibiri a gabar tekun yammacin Afirka, ta samu kanta a sahun gaba a jerin masu fama da basusska wanda ya kai kashi 109.7% na GDF.

Annobar COVID-19 ta yi wa ƙasar da ke dogaro da yawon bude ido mummunan illa, wanda hakan ya haifar da karuwar rance don dorewar tattalin arzikinta.

2. Mozambique (92.4%)

Mozambique, wadda ke fama da matsalar bashi tun daga shekarar 2016, ana binta bashin da ya kai kashi 92.4% na karfin GDP na kasar.

Duk da kokarin sake fasalin basussukan ta da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, ƙasar na ci gaba da tsunduma cikin kalubalan kasafi kudi saboda rashin tabbas na tattalin arziki.

3. Jamhuriyar Kongo (91%)

Jamhuriyar Kongo ta tara yawan basussuka da GDP da ya kai kashi 91% wanda ya samo asali ne sakamakon dogaron da take yi kan fitar da mai.

Kara karanta wannan

70% na fursunoni a Kano na jiran shari'a, suna samun ilimi a daure

4. Saliyo (82.6%)

Adadin bashin da ake bin kasar Saliyo ya haura zuwa kashi 82.6%, lamarin da ke nuni da kalubalen da wannan kasa ta yammacin Afirka ke fuskanta wajen farfadowa bayan tashe-tashen hankula.

5. Ghana (81.5%)

A kwanakin baya ƙasar Ghana ta sha yabo kan ci gaban tattalin arzikinta, yanzu ƙasar na fuskantar kashi 81.5% na basussuka da GDP..

Babban gibin kasafin kudi da basussukan waje sune suka jawo taɓarbarewar tattalin arzikin ƙasar, rahoton Bussines Day.

6. Mauritius (78.9%)

Mauritius, wanda take cibiyar hada-hadar kudi da yawon shakatawa, tana fama da kason basussuka da karfin tattalin arziki 78.9%.

Dole ne ƙasar ta daidaita tsakanin dorewar ci gaban tattalin arziki da magance hauhawar basussukan da take karɓowa domin tsare kasafinta na dogon lokaci.

7. Malawi (77.4%)

Duk da samun ci gaba a tattalin arziki, Malawi na fama da basussuka da suka kai 77.4% na ƙarfin tattalin arzikinta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka Farfesa tare da sace mutum 2 a wani sabon hari

Magance wannan ƙalubalen yana buƙatar tsari nagari da kula da kasafin kuɗi tare da saka hannun jari a sassa masu mahimmanci don ci gaba mai dorewa.

8. Angola (77.1%)

Angola, wacce ta dogara sosai kan mai, tana fama da basussuka da ƙarfin tattalin arziki da ya kai 77.1%.

Kasar dai na ƙoƙarin kawo sauye-sauyen tattalin arziki da kuma kula da basussuka don tunkarar rashin tabbas na farashin man fetur da kuma gina makoma mai karfin tattalin arziki.

9. Afirka ta Kudu (75.8%)

Afirka ta Kudu, ɗaya daga cikin masu karfin tattalin arziki a Afirka, ba ta tsira daga tarin basussuka ba domin ya kai 75.8%.

Matsalolin tsare-tsare, rashin tabbas na siyasa, da kuma illolin da cutar korona ta haifar ya sa dole ƙasar ta haɗa karfi da karfe wajen farfaɗo da arzikinta.

10. Senegal da Ruwanda (72.1%)

Kasashen Senegal da Rwanda sun haɗu wuri ɗaya a kashi 72.1% na basussuka da GDP, wanda hakan na nuni da kalubalen da wadannan kasashe ke fuskanta wajen ci gaba.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan fasinjoji sun kone kurmus a wani hatsarin mota a Kogi

11. Morocco

Maroko ta samu kanta a matsayi na 17 a duniya a cikin kasashen da suka fi ciyo basussuka daga asusun lamuni na duniya IMF, a cewar wani sabon rahoto da shafin binciken kudi na “Insider Money" ya wallafa.

Wannan rahoton ya sanya Maroko ta shiga cikin jerin sauran ƙasashen da ke fama da bashin IMF, rahoton jaridar Morocco News.

Waɗanda ba za su ci rancen karatu ba

A wani rahoton kuma Fadar shugaban ƙasa ta ce shirin bada lamuni ga ɗaliban Najeriya zai taimaka wajen ganin an samu ci gaba a harkar ilmi a ƙasar nan

Sai dai, ba dukkan ɗalibai ba ne suka cancanci wannan shiri da aka yiwa laƙabi da wanda ba a taɓa yin irinsa ba a tarihi, mun tattaro waɗanda ba za a ba rancen ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel