Budurwata rabuwa da ni tayi lokacin da rasa aikina a Banki, Matashin da ya koma aikin direba

Budurwata rabuwa da ni tayi lokacin da rasa aikina a Banki, Matashin da ya koma aikin direba

  • Saurayi ya bayyana abinda budurwarsa tayi masa lokacin da ya rasa aikinsa
  • Ya bayyana yadda ya kwashe shekaru biyu yana neman aiki bayan rasa aikinsa a banki
  • A cewarsa, wannan yayi sakamakon rashin budurwarsa

Accra - Wani matashin direba ya bayyana mugun halin da ya shiga na rashin kudi da kuma rashin budurwarsa lokacin da ya rasa aikinsa a bankin Beige a Ghana.

A Agustan 2018, Bankin Ghana (BoG) ta janye lasisin Beige Bank da wasu bankunan kasar hudu.

Sauran bakunan sune uniBank Ghana Limited, Royal Bank Limited, Sovereign Bank Limited da Construction Bank Limited.

Matashin yanzu ya koma aikin direba.

Budurwata rabuwa da ni tayi lokacin da rasa aikina a Banki, Matashin da ya koma aikin direba
Budurwata rabuwa da ni tayi lokacin da rasa aikina a Banki, Matashin da ya koma aikin direba Hoto: Ride and Chat
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Sheikh Abduljabbar ya sake rikici da Lauyoyinsa a Kotu, Yace basu da cikakken ilimin kare shi

Yayin hirarsa da Ride/Chat, ya bayyana cewa ana gab da karasa masa girma wannan abu ya faru.

"Ina aiki da bankin Beige. Ana gab da kara min girma lokacin da kamfanin ya ruguje a 2018," yace.

Ya kara da cewa sai da kwashe shekaru biyu yana neman aiki kuma bai samu ba.

Ga bidiyon jawabinsa:

Wani babban malami ya ɗirkawa budurwa cikin shege daga zuwa neman addu'a

Wani babban malamin addinin kirista ya shiga hannun yan sanda bisa zarginsa da yi wa wata budurwa cikin shege.

Aminiya Hausa ta ruwaito cewa babban faston ya ɗirkawa budurwar yar shekara 16 ciki ne ta tsiya yayin da aka kaita ya mata addu'a a cocinsa.

Binciken yan sanda ya nuna cewa bayan ya tilasta mata yin amfani da ita a gida, ya kuma tasa ta zuwa kasuwa da daddare inda ya sake kwanciya da ita a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Sau biyar kenan, an ceci wani mutumin da ke kokarin kashe kansa a Abuja

Babban malamin na addinin kirista ya amsa laifin da ake tuhumarsa a kai da farko amma daga bisani yace addu'a kawai ya mata kamar yadda aka bukace shi ya yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel