Rabiu Kwankwaso ya bude asibitin kula da masu shaye-shayen kwayoyin farko a Najeriya

Rabiu Kwankwaso ya bude asibitin kula da masu shaye-shayen kwayoyin farko a Najeriya

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da asibitin kula da masu shaye-shaye
  • Tsohon Gwamnan na Kano ya bude asibitin ne a lokacin da ya cika shekara 65
  • Sanata Kwankwaso yace ya dade yana burin ya samar da irin wannan cibiya

Kano - A ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, 2021, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya bude asibitin kula da masu shaye-shaye.

Legit.ng Hausa ta samu labari Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da Amana Sanatorium, domin gyaran halin wadanda suka fada wa shan kwayoyi.

Punch tace Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zuba kayan aiki a wannan asibiti da aka bude. Akwai sashen kula da wadanda takaici ya yi masu yawa.

Bayan haka kuma akwai bangare da aka ware ga wadanda ke kokarin guje wa shan kwayoyi.

Read also

Gwamna Ganduje ya motsa siyasar Kano, ya taya Kwankwaso murnar kara shekara a Duniya

A karon farko a Najeriya

Wannan asibitin da aka bude yana kan babban titin Kano zuwa garin Wudil, jihar Kano. Shi ne farkon irinsa da wani mai zaman kansa ya bude a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amana Sanatorium Private Rehabilitation Clinic
Cibiyar gyara masu shaye-shaye da damuwa na Amana Sanatorium Hoto: tribuneonlineng.com
Source: UGC

Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi mulkin jihar Kano sau biyu a 1999 da 2011 ya kaddamar da asibitin a ranar da ya cika shekara 65 da haihuwa a Duniya.

Wannan cibiya ta musamman za ta taimaka wa masu fama da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da makamantansu, domin su iya gyara rayuwarsu.

Rabiu Musa Kwankwaso ya yi jawabi

Da yake jawabi a taron, Kwankwaso ya bayyana cewa ya dade yana burin ya samar da wani abu wanda zai amfani al’umma, har a gina irin wannan cibiyar.

Tsohon Ministan tsaron yace za a kula da masu shaye-shaye da suke neman canza hali a wannan cibiya, domin su samu damar cigaba da rayuwa da sauran jama’a.

Read also

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Wadanda suka halarci bikin kaddamarwar sun hada da Buba Galadima, Suleiman Hunkuyi, Farfesa Rufai Alkali, manyan ‘yan siyasa, har da wani malami.

Ganduje ya bada mamaki

A jiya ne aka samu labari yayin da ake tsakiyar rigingimu a APC, Gwamnan jihar Kano ya tura sakon taya murna ga Rabiu Kwankwaso kara shekara a Duniya.

Dr. Abdullahi Ganduje ya aika wa tsohon Mai gidansa Kwankwaso sakon taya shi murnar cika shekara 65. Amma wasu suna ganin da walakin, goro a miya.

Source: Legit

Online view pixel