Dr. Ahmad Gumi yace Kirismeti da Mauludi bidi’o’i ne a addinan Musulunci da Kiristanci

Dr. Ahmad Gumi yace Kirismeti da Mauludi bidi’o’i ne a addinan Musulunci da Kiristanci

  • Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana a kan bukukuwan Mauludi
  • Da farko Malamin yace babu wanda ya san asalin ranar da aka haifi Annabi SAW
  • Shehin Malamin ya bayyana Kirismeti da Mauludi a matsayin bidi’o’i a addini

Kaduna - Babban malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi rubutu, yace babu wanda ya san ranar haihuwar Annabawa.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi wa wannan rubutu da ya wallafa a Facebook take da ‘PROPHETS OF GOD: the hoax of their birthdates!’

Fitaccen malamin yake cewa babu wani Annabin Allah da aka san asalin ranar da aka haife shi.

A cewar Ahmad Mahmud Gumi duk kintace ne da sa rai kurum ake yi, saboda a lokacin da aka haife su, ba a adana tarihi kamar yadda ake yi a yau.

Read also

‘Yan wasan Kannywood sun kirkiri fim a kan rikicin Boko Haram a Arewacin Najeriya

Sai yanzu ne mutane suka damu da tarihi, suke rubutu ranar da aka haifi mutane. Gumi ya yi wannan magana ne a lokacin da ake Maulidin Annabi.

Dr. Ahmad Gumi
Jana'izar diyar Sheikh Ahmad Gumi Hoto: desertherald.com
Source: UGC

“A Injila, an ce an haifi Annabi Adam (AS) ne a rana ta shida, wanda ya zo daidai da nassin wani hadisi da yace an haife shi a ranar Juma’a bayan la’asar.”
“Idan muka zo lokacin Annabi Isa (AS), ruwayoyi sun ce an haifi shi ne a shekara ta 12 BC, amma ba a fadi ainihin ranar haihuwar ba.” – Ahmad Gumi.
“Wasu kiristoci suna ganin cewa bikin kirismeti da ake yi yana cikin kirkire-kirkiren arnan rumawa.”

Gumi yace haka abin yake a Islama domin abin da ya tabbata shi ne an haifi Annabi (SAW) a ranar Litinin, amma Larabawa ba su da ilmin adana kwanan wata.

Read also

Watanni 4 da sauya-shekar gwamna zuwa APC, PDP tace ana neman rusa mata hedikwata

Mauludi da Kirismeti; addini ko bidi'a?

“Asali ma an fara kirga kwanakin wata ne a mulkin Umar Khattab (RA). Don haka Mauludi da Kirismeti bukukuwa ne da aka kirkiro domin yaudarar al’umma.” - Gumi

Bugu da kari, malamin ya yi raddi a kan masu yin wadannan bukukuwa, yace ya kamata duk abin da za ayi, a dogara da hujjojin addini ba koyi da wasu dauloli ba.

Mauludin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

A gefe guda, an ji yadda 'yan darika da wasu mabiya suke shirya bukukuwa mauludi a Najeriya. Daga cikin su akwai jagoran darikar Tijjaniya, Dahiru Usman Bauchi.

A wajen bikin da ya shirya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi yace mutanen kasar nan suna shan wahala.

Source: Legit

Online view pixel