Rundunar Najeriya ta samu galaba a kan Boko Haram, sun kashe Sojojin ‘Yan ta’adda

Rundunar Najeriya ta samu galaba a kan Boko Haram, sun kashe Sojojin ‘Yan ta’adda

  • Sojojin kasan Najeriya sun hallaka ‘Yan ta’addan ISWAP da Boko Haram a Borno
  • Kakakin sojoji na kasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya fitar da jawabi
  • Hafsun Sojan kasa, Janar Faruk Yahaya ya jinjina wa dakarun bayan samun labari

Borno - Akalla ‘yan ta’addan kungiyar Islamic State West Africa (ISWAP) da Boko Haram takwas suka mutu a hannun dakarun sojojin kasan Najeriya.

A wata sanarwa da Onyema Nwachukwu ya fitar ta Facebook, yace rundunar Operation Hadin Kai ta kashe ‘yan ta’addan ne a yankin Arewa maso gabas.

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar da wannan jawabi ne a ranar Talata, 19 ga watan Oktoba, 2021.

Mai magana da yawun bakin sojojin kasan Najeriyar yace ‘yan ta’adda takwas aka hallaka a wurare biyu da aka kai hari a yunkurin kawo zaman lafiya.

Read also

'Yan sanda sun yi ram da baƙin haure 2 dauke da abubuwa masu fashewa cikin jakunkuna

Nwachukwu yace da karon farko an hallaka ‘yan ta’addan ne a sansanin sojoji na Forward Operating Base (FOB) da ke garin Wulgo, da ke jihar Borno.

Rundunar Najeriya
COAS, Faruk Yahaya Hoto: punchng.com
Source: UGC

Sojojin Kamaru sun bada gudumuwa

Rundunar hadin-gwiwa ta Operation HADIN KAI (OPHK) da wasu sojojin kasar Kamaru ne suka taka rawar gani wajen kashe ‘yan ta’addan a yankin Wulgo.

Rundunar sojojin kasan sun kai hari na biyu a kusa da sansanin bataliya ta 151, inda motar sojojin ta bi ta kan wasu bam-bamai da aka shimfida a hanya.

An yi nasarar babbake ‘yan ta’addan kurmus, kuma ana cigaba da shawagi da jiragen sama.

An karbe wasu kayan fada

Jami’in tsaron yake cewa ‘yan ta’adda hudu suka mutu a take. Bayan haka an samu makamai da suka hada da bindigar AK 47 da harsasai 50 masu mita 7.62.

Read also

‘Yan wasan Kannywood sun kirkiri fim a kan rikicin Boko Haram a Arewacin Najeriya

Jawabin yace shugaban hafsun sojoji na kasa, Laftanan Janar Faruk Yahaya ya yaba da kokarin sojojin kasan, ya kuma yi kira gare su da su kara maida hankali.

An fito da Sarkin Bungudu

Ku na da labari cewa kwanaki ‘Yan bindiga sun karbi Naira miliyan 20 a hannun iyalin Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru, amma suka ki fito da Mai martaban.

Kungiyar Miyetti Allah ta taka rawa wajen fito da Sarkin da aka yi garkuwa da shi a watan jiya. Rahotanni sun ce sai da aka kara masu wasu makudan kudi.

Source: Legit

Online view pixel