Na shirya tsaf don mika kaina ga hukumar EFCC dauke da bargo, fulo da kayan bacci - Fayose

Na shirya tsaf don mika kaina ga hukumar EFCC dauke da bargo, fulo da kayan bacci - Fayose

- Dr. Ayodele Fayose, ya ce mika kansa ga hukumar EFCC dauke da kayan baccinsa har da ma fulo da bargon rufa

- Hukumar EFCC na zargin Fayose da karbar akalla N1.3bn daga ofishin Sambo Dasuki, a gwamnatin Goodluck Jonathan

- Chief Femi Fani-Kayode, ya ce shi da wasu gwamnoni da mambobin jam'iyyar PDP za su raka Fayose har shelkwatar EFCC

Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Ayodele fayose, wanda wa'adin mulkinsa ya kare a daren ranar litinin, a safiyar nan ya ce zai mika kansa ga hukumar dakile cin hanci da rashawa da yiwa dukiyar al'umma zagon kasa EFCC a ranar Talata (yau) dauke da kayan baccinsa har da ma fulo da bargon rufa.

Duk wata kariya da Fayose ke da ita, ta kare ne tare da karewar wa'adin mulkin nasa, wanda kuma aka gayyace shi zuwa shelkwatar hukumar EFCC da ke Abuja don asa wasu tambyoti kan zargin da ake masa na karbar akalla N1.3bn daga ofishin mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan sha'anin tsaro, ta hannun ministan tsaro na cikin gida na wancan lokacin, Sanata Musiliu Obanikoro.

Fayose ya ce: "Zan kai kaina shelkwatar a ranar Talata, bana rokon kowanya bada belina. Ya rage ruwansu, idan sunso suyi duk abun da suka ga dama da ni, ni dai kawai su bani gadon da zan kwanta. Na riga na shirya kayan bacci na, bargo da fulo da kuma rigar katifa.

KARANTA WANNAN: Bakin alkami ya bushe: APC ba ta da 'yan takara a zaben 2019 na jihar Zamfara - INEC

Na shirya tsaf don mika kaina ga hukumar EFCC ba tare da jin tsoron komai ba - Fayose
Na shirya tsaf don mika kaina ga hukumar EFCC ba tare da jin tsoron komai ba - Fayose
Asali: Depositphotos

"Haka zalika na tanadi littafin Bible dina na turanci dana Yarabanci. Nina shirye nake. Babu wanda nake so ya damu da halin da zan shiga. Lalatattu ne kawai ke mutuwa ba adadi kafin ranar mutuwarsu."

Majiya daga bangaren Fayose, ta labarta mana cewa shugaban kungiyar gwamnonin PDP, zai samu rakiyar wasu gwamnoni da kuma mambobin jam'iyyar ta PDP.

Da ya ke jawabi, a taron liyafar da aka shirya don yiwa Fayose bankwana, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Chief Femi Fani-Kayode, ya ce shi da wasu gwamnoni da mambobin jam'iyyar PDP za su raka Fayose har shelkwatar EFCC.

Ya ce a lokacin da shima yake tsare a hannun hukumar a 2016, gwamnan mai barin gado ya kai masa ziyara tare da karfafa masa guiwa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel