Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

  • Daga karshe dai jami'an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa sun kama sanata Okorocha
  • A yau ne rahotanni suka karade kasar nan kan yadda jami'an suka mamaye gidansa, lamarin ya haifar da cece-kuce
  • Bayan dogon kai ruwa rana, an tafi da sanatan, kana an yi harbe-harbe da cin zarafin 'yan jarida a kofar gidan nasa

Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama Sanata Rochas Okorocha a gidansa ta tafi dashi.

Hukumar ta kutsa kai cikin gidan nasa ne bayan da aka ji karar harbe-harbe a wajen, kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya.

EFCC sun kama sanata Okorocha
Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa | nationalaccordnewspaper.com
Asali: UGC

EFCC ta kuma dage cewa dole ne ‘yan jarida su fice daga harabar gidan, tare da korar duk wanda ke gidan da karfi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an tsaro sun budewa magoya bayan Okorocha wuta a farfajiyar gidansa

Wani mai daukar hoto na gidan talabijin na Channels, Kabiru Owoyemi, na daga cikin wadanda aka kora a lokacin da aka kori manema labarai. An buge shi da bindiga a wuya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ki cin biri, an ci dila: Yadda sabon AGF ke da jikakkiyar tuhumar rashawa da EFCC

A wani labarin, mi’an sun kuma yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa ‘yan jarida daga wurin.

Idan za a tuna, an nada Nwabuoku ya maye gurbin Ahmed Idris a ranar Lahadi bayan dakatar da Idris da aka yi kuma yana hannun hukumar EFCC kan zarginsa da almundahanar kudi har N80 biliyan.

Amma rahoto daga EFCC ya bayyana cewa sabon AGF din ana tuhumarsa da laifukan rashawa. Read more: https://hausa.legit.ng/news/1471322-an-ki-cin-biri-ci-dila-yadda-sabon-agf-ke-da-jikakkiyar-tuhumar-rashawa-da-efcc/

Asali: Legit.ng

Online view pixel