Yanzu-yanzu: Fayose ya dira ofishin EFCC da jakan kayansa

Yanzu-yanzu: Fayose ya dira ofishin EFCC da jakan kayansa

Kamar yadda yayi alkawari, tsohon gwamna Ayodele Fayose ya dira ofishin hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, da jakan kayansa.

Tawagar hadimai da abokan siyasa na tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, sun dira ofishin EFCC na unguwar Wuse 2 dake birnin tarayya Abuja.

Fayose, wanda wa'adinsaa ya kare a yau na karkashin zargin karban N1.3bn daga ofishin Kanal Samo Dasuki ta hannun tsohon ministan tsaro, Musiliu Obanikoro.

Yanzu-yanzu: Fayose ya dira ofishin EFCC da jakan kayansa
Yanzu-yanzu: Fayose ya dira ofishin EFCC da jakan kayansa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fasinja ya fito da azzakarinsa, yayi istimna’I, ya shafawa dan jaririn wata fasinja maniyyi a baki

Ya isa ofishin ne tare da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da tsohon ministan sufurin sama, Femi Fani-Kayode.

Sanye da bakar riga mai rubutun "EFCC gani nan", ya ce: "Gani nan kamar yadda nayi alkawari cewa zan zo ranan 16 ga watan Oktoba, kuma kamar yadda na fadawa EFCC su saurari zuwa na."

"Da safen nan su zo gidana kuma ban yi tunanin hakan na da wni amfani ba."

Gwamnan jihar RIbas, Wike ya tofa albarkacin bakinsa inda yace: "Ya fadawa EFCC cewa zai mika kansa ranan 16 ga watan Oktoba. Saboda haka yan Najeriya su sani cewa da kansa ya zo nan ba tare EFCC sun ci mutuncinsa ba, shi yasa na kawo shi nan."

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng