Yadda Arzikin Aliko Dangote Ya Karu da Naira Tiriliyan 6 Cikin Wata 1 Inji Bloomberg

Yadda Arzikin Aliko Dangote Ya Karu da Naira Tiriliyan 6 Cikin Wata 1 Inji Bloomberg

  • Alkaluman da aka samu daga Bloomberg Billionaires Index sun nuna arzikin Aliko Dangote sun karu
  • Mai kudin na Afrika ya ba sama da $20bn baya a rahoton karshe da aka samu na manyan attajiran duniya
  • Dukiyar Dangote tayi wani irin tashi ne sakamakon kudin da Femi Otedola ya narka a kamfani simintinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Darajar hannun jarin kamfanin simintin Dangote ya nunku fiye da biyu kamar yadda Bloomberg Billionaires Index ya nuna.

A dalilin haka arzikin Alhaji Aliko Dangote ya karu zuwa fam $22bn a cewar Bloomberg.

Aliko Dangote
Aliko Dangote da Femo Otedola Hoto: Getty Images, Bloomberg
Asali: Getty Images

Femi Otedola ya daga Aliko Dangote

Abin da ya faru kuwa shi ne, Femi Otedola wanda mutumin Aliko Dangote ne, ya saye hannun jari masu tsoka daga simintin Dangote.

Kara karanta wannan

FAAN, CBN: Yadda muka yi da Sanata Ndume da ya kira ni a waya da dare - Okupe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Otedola wanda ya ba Dala biliyan 1.1 baya yana da kyakkyawar alaka da Alhaji Dangote.

Rahoton yace wannan lamari ya taimakawa mai kudin na Afrikan ya samu kudin da bai taba ganin irinsu a cikin kusan shekaru goma.

Meyasa Otedola ya shiga kamfanin Dangote?

Da yake bayanin hikimar sa kudinsa a kamfanin simintin abokin na sa, attajirin yace hakan zai ba su damar samun kudin kasashen waje.

Baya ga haka, a jawabin Otedola, an ji yana cewa ya sa kudinsa a hannun jarin ne ganin yadda Dangote suke bin ka’idoji wajen aikinsu.

Bugu da kari, mai kudin ya kafa hujja da kishin Afrika da yadda kamfanin yake biyan masu hannun jari riba cikin dalilan sa kudinsa.

Matsayin Aliko Dangote a Afrika

A shekarar bara, Dangote wanda hukumar EFCC ta ziyarci hedikwatar kamfaninsa shi ne na 111 a jerin attajiran da ke fadin duniya.

Kara karanta wannan

Atiku ya jefawa Gwamnatin Tinubu zafafan tambayoyi 5 kan bashin $3.3bn da aka ci

Zuwa yanzu da ake tattara rahoton nan, matsayinsa ya koma kimanin na 83 a ban kasa, Daily Trust ta fitar da wannan labari dazu.

Da $20.9bn a asusunsa, mutane 80 ne kurum suka fi Dangote kudi, mafi kyawun matsayin da ya samu kan shi a kusan shekaru biyu.

Johann Rupert v Dangote

A farkon Junairun bana aka samu labari mai kudin Najeriya Aliko Dangote shi ne na biyu a jerin manyan attajiran da ke nahiyar Afrika.

A shekarar 2022, sai da Dangote ya zama attajiri na 63 a duniya kuma na farko a Afrika, zuwa 2024 ne Johann Rupert ya doke shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel