"Ba Su Gane Shi Ba": Hamshakin Mai Kudi Femi Otedola Ya Shiga Motar Kasuwa a Wani Tsohon Bidiyo

"Ba Su Gane Shi Ba": Hamshakin Mai Kudi Femi Otedola Ya Shiga Motar Kasuwa a Wani Tsohon Bidiyo

  • Wani bidiyon attajirin dan kasuwa, Femi Otedola, a cikin wata motar molue da ta cika da mutane a Legas ya yadu
  • Duk da yanayin cunkoson wajen, Otedola ya zabi zama a wajen da fasinjoji ke zama, yana mai boye ko shi wanene da matsayinsa
  • Lamarin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya, suna masu jinjina kankan da kai da jajircewar attajirin ga al'umma

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani tsohon bidiyon attajirin dan kasuwa Femi Otedola a cikin babbar motar molue a Legas ya sake bayyana a soshiyal midiya.

Attajirin mai shekaru 61 wanda ya shahara wajen ayyukan jin kai, kamar yadda ya saba shiga mutane a kokarinsa na kyautata masu, ya zabi shiga wannan mota don jin yadda talakawa ke zirga-zirgansu cikinta a kullun.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu zai kawo karshen rashin tsaro a cikin watanni 6 Inji Janarorin Soja

Femi Otedola cikin motar molue
"Ba Su Gane Shi Ba": Hamshakin Mai Kudi Femi Otedola Ya Shiga Motar Kasuwa a Wani Tsohon Bidiyo Hoto: @bigsamblog/TikTok.
Asali: TikTok

Tsohon bidiyon Femi Otedola cikin Molue ya sake bayyana

Duk da matsayin na daya daga cikin attajiran Najeriya, Femi Otedola ya tafi ba tare da sauran fasinjojin da ke cikin motar sun gane shi ba. @bigsam ne ya wallafa bidiyon a TikTok.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da motar ta isa tashar tsayawa, Otedola ya tashi tsaye sannan ya fita zuwa inda zai je ba tare da hayaniya ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@ibrahimbolaniyi ya yi martani:

"Ranar zagayowar haihuwar Femi Otedola ne sannan yana so ya yi wa duk wanda ya gane shi alkhairi. Abun takaici babu wanda ya san shine, da gaske ne."

Tijani Muritala ya ce:

"Wannan izina ne ga masu girman kai cewa idan babu su abubuwa ba za su iya faruwa ba hatta Otedola zai ji babu dadi cewa duk da arzikinsa babu wanda ya gane shi."

Kara karanta wannan

Budurwa ta koka bayan ta ci karo da shinkafa a cikin cincin din 'mitifie' da ta siya a Legas

Sweet ta yi martani:

"Yaran masu kudi ne za su iya gane shi."

Investor_OJay ya ce:

"Hatta mutumin nan da ke sanye da farin riga ya ji a jikinsa wani abu Mai girma na KUSA da shi, amma bai da masaniya."

Mayokun yace:

“Ahhhh idan ni ne zan rike shi game.Ba zan bar shi ya tafi ba har sai ya taimaka mun.

Matashiya ta ga shinkafa a mitifie

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya bayan ta gano shinkafar dafa-duka a cikin cincin din 'mitifie' da ta siya N50.

Ta garzaya dandalin TikTok don baje kolin cincin din da abun da ya kunsa a ciki. Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel