Asalin Abin da Ya Jawo Hukumar EFCC Duro Mana da Rana Tsaka Inji Kamfanin Dangote

Asalin Abin da Ya Jawo Hukumar EFCC Duro Mana da Rana Tsaka Inji Kamfanin Dangote

  • Dangote Group ya fitar da jawabi da ya yi bayanin zuwan jami’an hukumar EFCC zuwa hedikwatarsu a Legas
  • Kamfanin ya ce tun farko an bukaci wasu bayanan kudi daga gare su, amma su ka bukaci a ba su karin lokaci
  • EFCC ba ta amince da bukatar Dangote ba, don haka sai ma’aikatanta su ka ziyarci babban ofishin kamfanin

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Kamfanin Dangote Group ya yi karin haske a kan wata ziyara da jami’an hukumar EFCC su ka kai masa kwanan nan.

Kamar yadda The Cable ta kawo rahoto, kamfanin ya tabbatar da lamarin, ya kuma yi karin bayanin matsayarsa a wajen binciken.

Babban ofishin Dangote
Kamfanin Dangote da EFCC ta ziyarta Hoto:estateintel.com
Asali: UGC

Kamfanin Dangote ya wanke kan shi

Kara karanta wannan

EFCC ta taso Emefiele a gaba, Dangote ya wanke kan shi daga zargin harkar Daloli

A jawabin da kamfanin ya fitar a ranar Asabar, Dangote Group ya ce kafin zuwan jami’an, an nemi su gabatar da wasu takardu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin Dangote group ya kuma ce sun nemi karin lokaci daga wajen hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya.

Dangote group ya ce jami’an EFCC suna neman wasu takardu ne da za su taimakawa hukumar wajen binciken kudin da su ke yi.

EFCC: Jawabin kamfanin Dangote

Channels ta ce bayan abin da ya faru a hedikwatarsu da ke Legas, kamfanin ya ga bukatar yi wa duniya duk bayanin da ya faru.

"Mun ga bukatar yi wa abokan huldarmu, masu ruwa da tsaki da sauran al’umma bayanin gaskiyar lamarin da ya auku.
A ranar 6 ga watan Disamba, 2023, mu ka samu takarda ana bukatar duk bayanan kudin kasar waje da CBN ya ba mu daga 2014 zuwa yau.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi abin da yake hana Bola Tinubu barci da kyau a Aso Rock Villa

Mun fahimci an tura irin wannan wasika ga sauran kamfanoni 51 ana bukatar wadannan bayanai na tsawon lokacin nan."

- Dangote Group

EFCC ba ta ba Dangote karin lokaci ba

Dangote ya nemi dalilin da za a nemi wannan bayani kuma ya bukaci karin lokaci domin tattara bayanan lissafin kudin shekaru 10.

EFCC ba su amince da karin lokacin ba, su ka bukaci samun wannan bayanai a lokacin da aka yanke, don haka su ka zo da kan su.

Jawabin kamfanin ya ce a masaniyarsu, babu doka da aka saba, kuma za su cigaba da ba EFCC hadin-kai a gudanar da binciken.

Dangote zai yi karin bayani a EFCC

Ana da labari EFCC ta na binciken abubuwan da su ka faru a CBN ne a lokacin Mista Godwin Emefiele yana kan kujerar gwamna.

Yanzu hukumar binciken ta bukaci zama da manyan shugaban kamfanin nan Dangote.

Asali: Legit.ng

Online view pixel