'Yan fashin daji ne ke kewaye da mu, Al'ummar Kaduna sun koka
- Kungiyar cigaban katafawa a jihar Kaduna ta koka kan yadda ta ce ana neman karar da su baki daya
- Shugaban kungiyar, Dr Samuel Achie, ya ce babu shakka kewaye suke da 'yan bindiga kuma suna neman dauki
- A cewarsa, daga farkon watan Augustan shekarar nan zuwa yanzu, an halaka a kalla rayuka arba'in da daya a yankin
Kaduna - Kungiyar cigaban katafawa ta jihar Kaduna, ACDA ta koka da yadda 'yan fashin daji suka kewaye yankunansu.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, shugaban kungiyar, Dr. Samuel Achie, wanda ya yi jawabi a madadin mazauna yankin, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kasashen ketare da su kawo musu dauki.
Achie ya kara da cewa dubban katafawa an fatattake su daga inda suka tashi kaka da kakanni kuma suna rayuwa yanzu a matsayin 'yan gudun hijira ba tare da wani tallafi daga gwamnatin jihar ba.
"A madadin jama'ar Atyap masu son zaman lafiya, mun kushe hare-haren da ake kaiwa tare da kira ga jama'a da su kasance masu bin doka da kuma addu'a ga Ubangiji kan ya warware wadannan matsalolin."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya mika godiya ga mazauna yankin kan yadda suka hada sansanonin gudun hijira a Madachip da Zonkwa domin taimakawa 'yan gudun hijira daga yankuna daban-daban, Daily Trust ta ruwaito.
"Taimakon da ake samu a sansanonin na bayyana cewa akwai jama'a da kungiyoyi masu matukar tausayi wadanda suka damu da halin da katafawa ke ciki ta yadda suke iya bada gudumawa daban-daban tun bayan kafa sansanonin."
"Daga watan Augusta zuwa yanzu, an sheke mutum arba'in da daya a hare-hare daban-daban. Mutum 3 aka sheke a Gora Goda kuma aka kone mota 1, an kashe wata mata a gonar ta da ke Unguwan Jaba, mutum hudu a Abuyab, 1 a Manchong, 17 a Madoo da kuma gidaje da aka kone tare da wasu mutum 2 a gonakinsu da ke Kurmin Masara.
"A Apiyejim/Kibori kuwa, an kashe mutum 13 da suka hada da babban faston ECWA kuma an kashe su ne a hanyarsu ta zuwa Kafanchan. Da wadannan abubuwan, ina da kowanne dalili na sanar da katafawa cewa 'yan fashin daji ne suka kewaye mu.
"Muna kira ga kowa da a yi kokarin cetonmu kafin mu kare a kasar mu. Za mu cigaba da mika bukatarmu ta zaman lafiya ta hanyar addu'a ga Ubangiji."
Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai
A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Talata, ya ce jiharsa ta fara aikin naira biliyan goma na gina wurin kiwo ga makiyaya a jihar Kaduna.
Daily Trust ta ruwaito cewa, El-Rufai, wanda ya zanta da manema labarai yayin wani taro da jami'an jam'iyyar APC a sakateriya jam'iyyyar da ke Abuja, ya ce nan da shekaru biyu za a kammala aikin.
Gwamnan ya ce babban bankin Najeriya na CBN shi ya taimaka wa jihar da kudi har N7.5 biliyan domin samun nasarar aikin, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng