Renewed Hope ko Wahala: An Fara Dawowa Daga Rakiyar Tinubu Kan Tashin Kudin Fetur

Renewed Hope ko Wahala: An Fara Dawowa Daga Rakiyar Tinubu Kan Tashin Kudin Fetur

  • Bisa dukkan alamu, mafi yawancin mutane ba su ji dadinkarin kudin man fetur da aka yi a yau ba
  • Sai dai jama’a su ka ji litar man fetur a gidajen man NNPC a birnin tarayya Abuja ya kai N617
  • Gwamnatin Bola Tinubu ta cire hannu daga biyan tallafin fetur, hakan ya kawo canjin farashi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tun daga lokacin da aka ji farashin litar fetur a gidan man NNPC ya koma akalla N617 a Najeriya, wasu su ka fara yin ruwan salati.

Legit.ng Hausa ta bibiyi abin da jama’a ke fada a kafofin sadarwa na zamani, ta fahimci kusan kowa yana Allah-wadai da karin kudin fetur.

Sai dai ba a rasa wasu da ke ganin gwamnatin Bola Tinubu ta dauko gyara ne wanda yake da zafi.

Kara karanta wannan

Daga Ajiye Mukaminsa a APC, An Jibge Jami’an Tsaro a Gidan Abdullahi Adamu

Man fetur
Shugaban kasa a Kenya kafin fetur ya tashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gyara ko kuwa wahala?

Wani 'dan kasuwa mai suna Kabir Garba yake cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"'Yan Arewa dole fa sai kun yiwa Jagaban uzuri kamar yadda ku kaiwa me G(w)askiya, shi gyaran targaɗe dama haka yake"

Abubakar Muhammad Inuwa da yake magana a Facebook dazu, ya ce: “Babu Wani renewed Hope, Renewed Shege ne.”

Ya ce:

“Da na Yarda MANJO ne ya dasa nakiyar baba Bola ya tashe ta, amma yanzu na fita.”

Baba Bala Katsina kuwa ya ce:

“Kun dai ga inda ‘masana’ su ka kai mu ko?”

Abin sai da salati!

Wani kuwa ya na mai salati, ya rubuta:

“Innalillahi wa inna ilaihi rah un!!! Farashin litar man fetur ya tashi daga N539 zuwa N617 a gidajen mai na NNPC da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Farashin Litar Man Fetur Ya Ƙara Tashi a Najeriya, Ya Haura N600 a Gidan Man NNPCL

Allah kawa talaka mafita.”

Muhammadu Buhari: Duk wanda ya tuna bara

Agba Jalingo ya nuna tun da fetur ya koma N617, babu mamaki nan gaba kadan mutane za su fara kewan Muhammadu Buhari.

Ahmad Ganga wanda yana cikin kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu, ya nuna da sake, har ya rubuta a shafinsa cewa ya cire Adekunle daga sunansa.

Matashin ya na neman jifar da hular da ya saba sanyawa mai dauke da tambarin Shugaba Tinubu.

"Na cire Adekunle daga suna na daga yau."

Can ya ce:

“Direba nan ya isa. Tsaya in sauka kawai. Na yafe sauran canjin

'Yan Twitter sun caccaki Jagaban

Labari mai zafi: Litar man fetur a NNPP yanzu ya kai N617. Ina fatan ku na cin moriyar ‘renewed shege’?

- @NEFERTITI

Kwamred Abiyos Roni ya koka game da yadda litar man fetur ya lula, sannan tsadar abinci ya karu zuwa 22.97%, amma za a rabawa talakawa N8000 kacal.

Kara karanta wannan

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

Wani mai suna Chally_001 a Twitter, ya yi lissafin cewa N8000 da za a ba talaka kyauta bai fi ya saye lita 12.9 na fetur ba.

“Renewed Shege”

Inji Sani Waspapping

Talaka a halin Wayyo Allah

Ku na da labari 'Yan majalisa za su samu masu bada shawarwari fiye da 2, 700 da za su rika karbar kusan N1m a wata, manya sun cigaba da bushasha.

Bayan haka Shugaban kasa da Ministoci na da tulin Hadimai bayan Biliyoyi da za a kashe a abinci da zirga-zirga a lokacin da talaka yake cikin matsi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel