"Ku Rika Duba Litattafan Yaranku": Wata Mata Ta Saki Hotunan da Ta Gani

"Ku Rika Duba Litattafan Yaranku": Wata Mata Ta Saki Hotunan da Ta Gani

  • Wata yar Najeriya ta shawarci iyaye su yi taka tsan-tsan yayin da ta wallafa Hotunan da ta gano a litattafan karatun kananan yara
  • Shafin littafin da ta wallafa ya yi bayani kan rayuwar iyali kuma an yi amfani da Hotuna kala daban-daban domin nuna kashe-kashen iyali
  • Yayin da wasu suka yi fatali da ankararwan matar, wasu na ganin wannan batu ne mai girma da ya kamata iyaye su sanya ido a kai

Wata mata 'yar Najeriya ta garzaya shafin sada zumunta domin ankarar da mutane irin Hotunan da ake sanya wa a cikin litattafan karatun ƙananan yara.

Ta bayyana cewa Hotunan da ake sanya wa da nufin fahimtar da yara abinda ake nufi abun dubawa ne da taka tsan-tsan ga iyaye.

Karatun yara.
"Ku Rika Duba Litattafan Yaranku": Wata Mata Ta Saki Hotunan da Ta Gani Hoto: Omenka2Hot/Facebook
Asali: Facebook

A shafinta na dandalin Facebook, Omeka2hot, ta shawarci iyaye da masu riƙe da kananan yara su riƙa ɗaukar litattafansu na karatu su bincika abinda ke ciki baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

Matar ta rubuta cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dan Allah ku riƙa ware lokaci ku buɗe littafin karatun yaranku shafi bayan shafi ku duba abinda ke ciki saboda na gaza gane wace irin rayuwa muka koma a yanzu."

Hoton shafin da matar ta wallafa ya yi bayani dalla-dalla cikin Hoto kan kashe-kashen iyalai.

Na farko a cikin Hotunan, ya nuna mata da miji da kuma 'ya'yansu guda biyu yayin da Hoto na biyu ke ɗauke iyalin da ya kunshi kakanni da jikoki.

Hotuna biyu na ƙarshe sun nuna iyaye maza biyu da ɗa guda ɗaya da kuma iyaye mata biyu, su ma tare da ɗa guda ɗaya a matsayin wani kashin iyali.

Mutane sun maida martani

Agu Prettyjane ta ce:

"Muna da rabe-raben iyalai biyu, Nuclear Family, watau Uba da mata da 'ya'yansu da kuma Extended Family, mai haɗe da kakanni da jikoki, waɗannan hotuna zasu taimaki yaro ya fahimta cikin hanzari."

Kara karanta wannan

"Ki Bar Bawan Allah Ya Huta": Bidiyon Wata Budurwa Da Saurayinta Suna Jin Daɗi a Dakin 'Hotel' Ya Girgiza Mutane

Chidera Fransisca ta ce:

"Ni naga wanda ya nuna yadda ma'aurata ke soyayya, mata ta kwanta yayin da mijin ya hau kanta... Ba zan iya tuna sauran abinda aka rubuta a littafin ba."
"Amma a zahirin gaskiya abinda suka rubuta bai dace da yaro ba, kuma littafin na ɗaliban ajin Firamare 2 ne."

"CBN Ya Tallafa Masa": Dalibin Sakandire Ya Zana N200 da Fensir Mai Kaloli

A wani labarin kuma Wani ɗalibin sakandire a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai, ya yi amfani da alƙalamin rubutun yara Fensir ya zana takardar N200.

Abraham Magu, ya yi wannan ƙwazo na zanen takardar N200 a wani hoto da yanzu haka ya ja hankalin mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel