Abin da manyan malamai suke fada game da rasuwar Sheikh Ahmad Ibrahim Bamba

Abin da manyan malamai suke fada game da rasuwar Sheikh Ahmad Ibrahim Bamba

  • A makon da ya gabata ne Duniyar musulmai tayi rashin babban shehin malami, Dr Ahmad Ibrahim Bamba wanda mutane suka fi sani da Ahmad BUK
  • Al’umma ta shaida tsoron Allah da ilmin wannan bajimin malamin hadisi da aka yi a Kano. Legit.ng Hausa ta tattaro abin da malamai su ke fada a kansa
  • Manyan malamai irinsu Farfesa Mansur Sokoto, Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu, Bn Othman, Bashir Aliyu Umar duk sun bayyana rashin da aka yi

Bayan an birne Ahmad Ibrahim Bamba, babban malami Dr, Muhammad Sani R/Lemo ya yi jawabi inda ya bayyana irin rashin da al’ummar musulmai suka yi.

Dr. R/Lemo ya yi wa mamacin addu’a, yace masu ilmin da ba za a maye gurbinsu ba, su na ta mutuwa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya tura tawaga Kano don gaisuwar ta'aziyyar Dr Ahmad BUK

A shafinsa na Facebook, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya yi addu’a a game da wannan rashi da aka yi, inda ya roki Allah ya sa Ahmad BUK a Aljannah.

Innalillahi wainna ilaihi Rajioon!!

Dr. Ibrahim Disina yace:

“Mutuwar malami babbar musifa ce. Innalillahi wainna ilaihi Rajioon!! Allah ka jikan Dr Ahmad Ibrahim Bamba Kano!! Allah ya kai haske kabarinka kamar yadda ka haska zukatan Mutane da hasken Hadisai!!!

Mutuwa Rigar Kowa

Irin wannan shi ne abin da Dr. Kabir Asgar ya rubuta a na sa shafin na Facebook a ranar Juma’a.

“Mutuwar malamai tana daga cikin babbar jarawabar da Allah ke yi wa bayinsa. Allah Ubangiji ya gafarta wa Dr Ahmad Ibrahim BUK. Allah ya sa mutuwa hutu ne. Allah ya sa aljanna ce makomarsa.”

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari, Gwamnoni, Ministoci sun yi ta'aziyyar Sheikh Ahmad Bamba

Ahmad Ibrahim Bamba
Malamin hadisi, Sheikh Ahmad Ibrahim Bamba ya rasu Hoto: muhammadsadis/Drmansursokoto
Asali: Facebook

Kabir Asgar yace dandazon mutanen kwarai wajen jana’izar mutum su na cikin alamun kyakkyawar cikawa, kuma Marigayin ya dace da hakan.

A hudubar Juma’ar da ya yi a makon jiya, Mohammed Bn Othman ya bayyana haduwar karshe da ya yi da malamin a lokacin da yake a kan gadon asibiti.

Mansur Sokoto ya yi wa Sheikh Dr. Ahmad Ibrahim BUK addu’a, ya bayyana yadda dattijon malamin ya dauko shekara da shekaru wajen karantarwa.

DR. AHMAD BAMBA (BUK): RAYUWA MAI TARIN ALBARKA

"Allah ya karbi hidimar da kayi wa hadisan Manzon Allah S.A.W. Allah ya baka ladan ilmantar da al'umma. Tabbas an shuka alheri. Albarkar rayuwa ta bayyana. Sai dai addu'ar Allah ya karba. Ameen. "

Asali: Legit.ng

Online view pixel