Kishi ya tashi ana tsakiyar biki yayin da wani Banufe ya auri ‘Yan Matansa 2 a lokaci 1

Kishi ya tashi ana tsakiyar biki yayin da wani Banufe ya auri ‘Yan Matansa 2 a lokaci 1

  • Ana ta labarin Mohammed Alfa Mohammed a kafafen sada zumunta a dalilin auren da ya yi da mata biyu yau
  • Alhaji Mohammed Alfa ya angwance da matansa - Adama Ahmad Mohammed da Aisha Ismail Mohammed
  • An ga kishin daya daga cikin amaren wannan Bawan Allah yayin da ake rawa a wajen bikin da aka yi a Bida

Niger - Wani Mohammed Alfa zai angwance da matansa biyu a lokaci guda Malama Adama Ahmad Mohammed da Malama Aisha Ismail Mohammed.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ana yin wannan gagarumin aure ne a garin Bida, jihar Neja.

Abin da ya sa ake labarin wannan aure shi ne angon zai auri mata biyu a lokaci guda. A addinin musulunci babu laifi namiji ya tara mata har hudu a aure daya.

An fara biki tun ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, inda aka yi taron mata a gidan daya daga cikin amaren a unguwar Low Cost a garin Bida, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano ta rikide, a yau Kwankwaso zai aurar da ‘Diyar cikin abokin adawarsa, Shekarau

A jiya Alhamis aka yi irin wannan bikim a gidan Alhaji Ahmad Mohammed Baba a unguwar Edogifu. A kowane taro an yi ta cashewa da wakokin Nufawa.

Wni Banufe ya auri ‘Yan Matansa 2
Mijin mata biyu Hoto: Twitter/lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda katin bikin ya nuna an fara aurawa Mohammed Mohammed Alfa sahibarsa Adama Ahmad Mohammed ne a yau Juma’a da safe a gidan iyayenta.

An shafa fatiha a ranar Juma'a

Bayan sallar Juma’a sai aka sake daurawa wannan Ango aure da dayar sahibar ta sa, Aisha Ismail Mohammed. Hakan ya sa ya tabbata a matsayin mai mata biyu.

A gobe Asabar ne za a shirya liyafa ta musamman tare da bikin nuna al’adun gargajiya. Za a kira manyan mawaka da ake ji da su a kasar Nufawa domin su yi wasa.

A karshe kuma za a yi wa’azi a ranar Lahadi da nufin tunatar da ma’aurata a game da hakkokin zaman aure. Sheikh Maan Baagi Agaie ne zai gabatar da wa’azi.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai kare ka: Na san matsalar Mambilla, a ba ni shekara 1 a ga canji inji Sabon Minista

A wani bidiyo da yake yawo a Twitter da Instagram, an ga kishin amaren ya fara tashi yayin da Alhaji Mohammed Alfa ya rike su domin su yi rawa a wajen biki.

Kwankwaso ya bada auren 'Yar Shekarau

A yammacin Alhamis, 23 ga watan Disamba, 2021, aka samu labarin cewa Sanata Ibrahim Shekarau zai aurar da 'yarsa, Halima (Amira) Ibrahim Shekarau.

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ne ya zama waliyyin Amira Ibrahim Shekarau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel