Dakarun Soji Sun Damke ‘Yan Ta’adda 79, Masu Taimaka Musu da ‘Yan Matan Chibok 2, DHQ

Dakarun Soji Sun Damke ‘Yan Ta’adda 79, Masu Taimaka Musu da ‘Yan Matan Chibok 2, DHQ

  • Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ta yi ram da ‘yan ta’adda 79 da masu hada kai da su a Arewa maso Gabas a makwanni biyu da su ka gabata
  • Darektan watsa labaran soji, Musa Danmadani, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taro da su ka yi a Abuja ranar Alhamis
  • A cewarsa, rundunar ta samu nasarar ragargazar ‘yan ta’adda da dama tare da ceto wasu ‘yan matan makarantar Chibok guda biyu

FCT, Abuja - Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ta samu nasarar kama fiye da ‘yan ta’adda 79 da masu taimaka musu a yankin Arewa maso Gabas a cikin makwanni biyu da su ka gabata, Premium Times ta rahoto hakan.

DanMadami
Dakarun Soji Sun Damke ‘Yan Ta’adda 79, Masu Taimaka Musu da ‘Yan Matan Chibok 2, DHQ. Hoto daga @dhq
Asali: Twitter

Musa Danmadami, darektan yada labaran soji wanda manjo janar ne, ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis a wani taro na ko wanne mako da ake yi don bayyana ayyukan sojin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Danmadami ya ce rundunar sojin kasa da sama ta samu nasarar ragargaje wasu ‘yan ta’addan, inda ta ceto wasu ‘yan matan makarantar Chibok a lokacin.

A cewarsa, ‘yan matan Chibok din guda biyu sun hada da Yana Pogu da Rejoice Senki wadanda aka ceto su tare da yaransu.

An ceto su ne a kauyen Bula Davo da ke karamar hukumar Bana a Jihar Borno da kuma kauyen Kawur da ke karamar hukumar Konduga a Borno tare da mutane 12 da aka yi garkuwa da su.

Danmadami ya sanar da manema labarai cewa rundunar ta kama ‘yan Boko Haram 29 da masu yi wa ‘yan ISWAP safarar kayan masarufi a wurare daban-daban.

A cewarsa, an kwace manyan buhunhunan busasshen kifi guda 50, buhunhuna biyu na soyayyen nama, jarkoki 55 na fetur, kudi Naira miliyan 2.4 da sauran abubuwa.

Ya kara da cewa rundunar ta kama wani da ake zargin yana hada makamai a kauyen Gorom da ke karamar hukumar Monguno a Jihar Borno.

Ya bayyana yadda aka kama mutane shida da ake zargin masu kai labari ne ga ‘yan ta’adda da kuma wasu ‘yan kasar waje da aka kama a wurare daban-daban.

Rundunar ta kwace bindiga kirar AK47 guda shida, AK47 magazines guda 14, bindigar HK daya, G3 daya, shanu 285 da galan takwas ba fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel