Yadda ‘Yar aiki ta hallaka mahaifiyar tsohon Gwamna saboda ta saci N100, 000 da agogo

Yadda ‘Yar aiki ta hallaka mahaifiyar tsohon Gwamna saboda ta saci N100, 000 da agogo

  • ‘Yan Sanda sun yi ram da Miss Dominion Okoro wanda ake zargi da laifin kashe Maria Igbinedion
  • Wannan budurwa ta shaidawa Duniya cewa ita ta kashe mahaifiyar tsohon gwamna Lucky Igbinedion
  • ‘Yar aikin, Dominion Okoro ta rotsa kan wannan tsohuwa ne cikin dare domin ta dauke mata kudi

Edo - A ranar Talata, 21 ga watan Disamba, 2021, wata ‘yar aikin gida mai suna Dominion Okoro ta amsa laifinta na kashe Madam Maria Igbinedion.

Wannan budurwa mai shekara 25 a Duniya ta hallaka Maria Igbinedion, watau mahaifiyarsu tsohon gwamnan jihar Edo, Cif Lucky Igbinedion.

Jaridar Punch ta rahoto Dominion Okoro ta na bada labarin yadda ta aika wannan tsohuwa barzahu.

Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya sun cafke Okoro a kauyensu a Kalaba, jihar Kuros Riba, inda ita kuma ta amsa wannan laifi da ake zarginta da aikatawa.

Kara karanta wannan

Kwastam ta samu kudin da suka zarce abin da aka daurawa Hameed Ali ya yi a shekarar nan

Dominion Okoro tace ta rankwalawa marigayiyar kujera ne a kai yayin da ta ke barci. Tun daga nan tsohuwar mai shekara 85 ba ta dade ta na shurawa ba.

Mahaifiyar tsohon Gwamnan Edo
Dominion Okoro da Maria Igbinedion Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan sanda sun gurfanar da wanda ake tuhuma a babban ofishinsu da ke garin Benin. Tribune ta rahoto Okoro tana cewa ta sulale da N100, 000 daga gidan.

Baya ga kudi, rahoton yace wannan budurwa ta sace agogo da gwala-gwalai daga gidan tsohuwarsu Igbinedion da ke unguwar GRA, Benin, Edo.

Jawabin wanda ake tuhuma da laifi

“Na kashe mama ne domin in dauke mata kudi. Ba tayi mani laifin komai ba. Ta na barci da kimanin karfe 12:01 na daren ranar 2 ga watan Disamba, 2021, nayi amfani da kujera, na rotsa kanta, sai tayi ihu tana neman taimako.”

Kara karanta wannan

Wanda ya yi wa Buhari Minista a 1984 ya kawo shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro

“Babu kowa a gidan sai mai gadi, shi ma bai ji kukan na ta ba. Daga baya dai Mama ta mutu.”
“Na jira zuwa karfe 4:00 na safiyar 2 ga watan Disamba, 2021, kafin in bar gidan, dauke da kudinta N100, 000 da agogo da kayan ado.”
“Sai na tsere zuwa jihar Kuros Riba, daga baya jami’an ‘yan sanda suka cafke ni.” – Okoro.

Za a maka Okoro a kotu - CP Ogbadu

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edo, Phillip Ogbadu, yace sun sha wahala kafin su yi ram da wannan yarinya, ya yi alkawarin za a gurfanar da ita a gaban Alkali.

Surukin gwamna ya bar APC, ya shiga APC

A baya an ji shugaban kungiyar Buhari/Masari Door-To-Door 2019 a Katsina, Bishir Audi Kofar Bai, ya bada sanarwar barin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina.

Bishir Audi Kofar Bai yace da su aka sha wahalar kafa APC, amma gwamnatinsu ba ta tsinana masa komai ba tun daga shekarar 2015, don haka ya koma PDP.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Labarin Amare da Angwaye 10 da suka mutu daf da aurensu ko bayan biki

Asali: Legit.ng

Online view pixel