Surukin Gwamnan Katsina ya bar APC, ya fara kira ga mutane su dawo da PDP kan mulki a 2023
- Alhaji Bishir Audi Kofar Bai ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina
- ‘Dan siyasar wanda yace shi ‘danuwan matar gwamna ne, ya koma PDP saboda rashin adalcin APC
- Bishir Audi Kofar Bai shi ne ya jagoranci kungiyar Buhari/Masari Door-To-Door a zaben da ya wuce
Katsina - Alhaji Bishir Audi Kofar Bai ya bada sanarwar sauya-sheka daga jam’iyyar APC mai mulki, inda ya ce ya bi jam’iyyar hamayya ta PDP a Katsina.
Jaridar Katsina Post tace wannan matashi ya na ikirarin cewa shi kanin matar gwamnan Katsina ne.
Bishir Audi Kofar Bai ya sanar da Duniya ya bar APC a gaban daruruwan ‘ya ‘yan jam’iyyar adawa da magoya baya a ranar Asabar, 18 ga watan Disamba, 2021.
Rahoton yace hakan ya zo daidai lokacin da PDP ta kaddamar da shirin yi wa ‘ya ‘yanta rajistan zamani a sakatariyarta a karamar hukumar Birnin Katsina.
Audi Kofar Bai : Da mu aka yi wahala a baya
Baya ga zamansa na ‘danuwan matar gwamna, Bishir Audi Kofar Bai yace shi ne shugaban tafiyar nan ta Buhari/Masari Door-To-Door a zaben 2019 da ya wuce.
Da yake bayanin dalilin ficewarsa daga APC da ya yi wa hidima a baya, Alhaji Bishir Audi Kofar Bai yace jam’iyyar ba ta da adalci, yace gumin da suka yi duk a banza.
Wannan ‘dan siyasa yace ba ayi la’akari da kokarin da suka yi wajen kafa APC a jihar Katsina da ma kasa baki daya ba, yace gwamnati ba ta taimake shi da komai ba.
A jawabinsa na farko ga jama’a a matsayin ‘dan PDP, Audi Kofar Bai ya yi kira ga jama’a su dage wajen ganin jam’iyyar APC ta sha kashi a babban zabe mai zuwa na 2023.
Audi Kofar Bai ya roki jama’an Katsina su yi kokarin ganin PDP ta dawo kan mulki a jihar. Tun 1999 jam’iyyar PDP ke rike da jihar ta Katsina, sai a 2015 lamarin ya canza.
An yi wa Alhaji Bishir Audi rajista, kuma ya nunawa Duniya katinsa na zama cikakken ‘dan PDP.
An ci amanar Tinubu a APC?
Kwanan nan aka ji cewa daya daga cikinmanyan ‘Yan Buhariyya a kudancin Najeriya, Osita Okechukwu, ya karyata littafin Bisi Akande da aka kaddamar a Legas.
A cewar Okechukwu, Bola Tinubu ya taimaka wajen ba Muhammau Buhari nasara, amma babu wata yarjejeniya da aka yi na za a ba shi mataimakin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng