Yadda maras hannu ta zama gangariyar tela a Abuja, ta fi masu hannu iya dinka kaya

Yadda maras hannu ta zama gangariyar tela a Abuja, ta fi masu hannu iya dinka kaya

  • Wata matashiya da ta rasa hannunta a lokacin da take sakandare tana rayuwarta lafiya kalau a yau
  • Da aka yi hira da ita, Miss Lucy tace yanzu ma ta fi kokari a kan lokacin da take da hannuwa biyu
  • Wannan Baiwar Allah tana sana’ar dinki duk da cewa da hannu daya take amfani da keken-dinki

Abuja - Lucy Akogo tela ce wanda ta ke aiki a birnin tarayya Abuja. Abin ban sha’awa game da wannan Baiwar Allah shi ne hannu daya take da shi.

Mutane suna mamakin yadda Lucy Akogo take murza keken dinki, duk da hannunta guda ba ya aiki. Abin da wasu masu hannuwan sam ba za su iya ba.

Akogo ta yi hira da BBC Pidgin News, ta bada labarin yadda mutane suke kura mata idanu a duk lokacin da suka hange ta a lokacin da take dinki a shago.

Read also

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

Idan kuwa aka ci karo da Akogo a hanya, ana mamakin wannan mai hannu guda da ta zama tela.

Wasu lokutan da gan-gan ake kawowa Lucy Akogo dinki domin kawai su gwada iyawarta. Ita kuwa sai ta rangada masu dinkin da sai sun bude baki.

Tela mai gundulmi
Lucy Akogo a bakin aiki Hoto: BBC Pidgin News
Source: Facebook

Lucy Akogo ta yi abubuwa da dama

Baya ga dinkin tufafi, Akogo ta bayyana cewa ta iya abubuwa da yawa. Saboda tana son gayu, matashiya da kanta take rangada kwalliya a fuskarta.

A hirarta da BBC Pidgin News, Lucy Akogo ta bada labarin yadda ta rasa hannuwa da kuma irin kokarin da aka yi na ganin ba a yanke mata hannun ba.

Wannan mata tace ta rasa hannuwanta ne a shekarar 2008 wajen buga kwallon kafa a sakandare.

Read also

Da dumi-dumi: Bayan shafe kusan watanni hudu a hannunsu, yan Boko Haram sun saki ma'aikacin gwamnatin Yobe

An yi ta kokarin ayi mata aiki domin hannun ya dawo daidai, amma shekara sama da goma kenan babu wata nasara, don haka ta bar lamarin ga Ubangiji.

Ganin ta kai an datse mata hannu ne aka ba Akogo shawarar ta zama tela. Da so samu ne, telar za ta so a ce ta zama jami'ar sojar ruwa, wannan shi ne burinta.

A kwanakin baya aka ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi wani rubutu kwanakin baya, inda ya kawo dalilan mace-macen aure a Arewacin Najeriya.

Aminu Ibrahim Daurawa yace zafin kishi da yawan sa-bakin iyaye suna cikin abubuwan da ke sa ma’aurata su rabu, sauran dalilan sune talauci da larurar lafiya.

Source: Legit

Online view pixel