Bidiyon yadda Daliban Jami’a suka tsuguna har kasa, suna bada hakurin rashin shiga aji

Bidiyon yadda Daliban Jami’a suka tsuguna har kasa, suna bada hakurin rashin shiga aji

  • An ga bidiyon wasu daliban jami’ar Afe Babalola suna dukawa a kasa
  • ‘Yan makarantar sun baje suna bada hakuri saboda ba su shiga aji ba
  • Mutane sun yi ta sukar jami’ar, suka ce ta zama makarantar firamare

Ado Ekiti - Bidiyon wasu daliban jami’ar Afe Babalola suna tsugunawa, suna bada hakuri ya jawo mutane da-dama suna ta magana a shafin sada zumunta.

A wannan bidiyo da @instablog9ja suka wallafa a Instagram, an ga ‘yan jami'ar sun sunkuya, suna neman afuwar shugaban jami’ar, Smaranda Olarinde.

Za a iya ganin Farfesa Smaranda Olarinde tana yi wa wadannan dalibai da suka yi laifi fada.

@instablog9ja da suka wallafa bidiyon suka rubuta: “Daliban Jami’ar Afe Babalola sun tsuguna, suna bada hakuri na kin shiga aji.”

Mutane a kafafen sada zumunta suna ta tofa albarkacin bakinsu har suna kiran jami’ar ta Afe Babalola da makarantar sakandare ko ma a ce firamare.

Read also

Dalibai sun yo hayar ‘yan daba domin su lallasa malamansu, an jikkata wasu

Jami’ar Afe University
Jami’ar Afe Babalola Hoto: www.abuad.edu.ng
Source: UGC

Abin da mutane suke cewa

@ruby.o yake cewa:

“Ba su so ayi asarar kudin makarantar da iyayensu suka biya ne.”

@poshest_hope ya rubuta:

“Makarantar sakandare ce kurum.”

Shi kuma @justdamz_ ya rubuta:

“Wannan makarantar firamare ce ka ji. Saura kuma ayi masu duka saboda sun goge kayansu da takalmansu”
“Wannan makarantar firamare ce ta manyan dalibai. Na tabbata suna yin taron PTA.” Inji @comedianxtreme.

@thesehoesistrife ya rubuta:

“Na tsani irin wannan abin. Irin wannan dabi’ar da halin cin mutunci ya jawo ‘yan sanda suke cin zarafin mutane. Ba abin dariya ba ne.”

Mai shekara 91 ya zama SAN

Kwanakin baya aka ji Farfesa Ajagbe Toriola Oyewo ya kai mukamin SAN yana da shekaru 91. Ajagbe Oyewo ya yi digirin farko a 1960, ya kammala PhD tun a 1983.

Read also

Matsalar tsaro: Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

Ajagbe Toriola Oyewo mai shekara 91 a Duniya, yana cikin wadanda za a rantsar a matsayin sababbin SAN.

Source: Legit

Online view pixel