Latest
A jiya Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta taka muhimmiyar rawar gani wajen dakusar da tsanani na ta'addancin Boko Haram a jihar Borno wanda da tuni wani labari ake ji ba wannan ba.
Fusatattun mazauna yankin Sharada Malam a garin Kano sun kai wa tawagar yanke wuta da karban kudaden shiga na hukumar Kano Electricity Distribution Company (KEDCO) hari. Kakakin KEDCO, Mohammed Kandi ne ya bayyana hakan.
Majalisar dattawa a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwama ta amince da samar da sabbin makarantun gaba da sakandare 10 a fadin kasar. An yanke shawarar ne bayan yan majalisar dokoki sun samu rahoton kwamitin majalisar dattawa kan hakan
“Amma abin takaici har yanzu babu wani martani daga fadar, kuma babu wanda ya cike gurbin limancin, don haka muna jin zafin wannan mataki, kuma muna yi ma mahukunta tuni da su duba kukanmu da idon tausayi.” Inji kungiyar.
Hukumar sojin kasa ta Najeriya ta yi karin haske tare da bayar da tabbaci kan adadin rayukan dakarun soji da suka salwanta a sanadiyar harin mayakan Boko Haram da ya auku cikin garin Metele na jihar Borno makonni 2 da suka gabata.
Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin ofishin babban akanta na kasa,Oise Johnson ne ya bayyana haka a ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, inda yace an gudanar da taron kasafta kudin ne a jahar Kaduna, inda yace an samu karin naira b
Rundunar Yansandan jahar Edo ta sanar da cafke wani karamin yaro dan shekara goma sha shida mai suna Zakaria Chiahemba akan zarginsa da halaka uwardakinsa mai suna Rejoice Odogwu mai shekaru hamsin da uku a rayuwa.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa yan ta’addan Boko Haram sun fara amfani da jirage marasa matuka wajen kai farmaki a kan cibiyoyin tsaro na sojojin kasar. Hukumar sojin ta ce ta kula cewa wasu na taimakawa yan ta'addan.
Wani da ake zargin jami’in ya sanda masu yaki da yan ta’adda ne (SARS) ya hari wani jami’in kula da cunkoso a titi na jihar Lagas wato State Traffic Management Authority (LASTMA) har lahira. Lamarin ya afku ne a ranar Laraba.
Masu zafi
Samu kari