Rudunar soji ta kai ziyarar ta’aziya ga uwargidan sojan da ya mutu (hotuna)

Rudunar soji ta kai ziyarar ta’aziya ga uwargidan sojan da ya mutu (hotuna)

Rundunar sojin ajeriya a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba ta kai ziyarar jaje da ta’aziyya ga wata mata mai suna II Sakaba, matar jarumin sojan da ya mutu, Lieutenant Colonel Ibrahim Sakaba.

Legit.ng ta tattaro cewa rundunar ta bayyana hakan a shafinta na Twitter a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba, cewa tawagar rundunar karkashin jagorancin Birgediya Janar SI Igbinomwanhia.

Ga yadda hukumar ta wallafa a shafinta:

Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa hukumar Sojin Najeriya ta ce dakarunta guda 39 suka rasu a harin kwana-kwanan nan da mayakan Boko Haram suka kai a Metele ba 188 kamar yadda kafafen yadda labarai suka ruwaito ba.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 7 da Buhari ya fadi a Maiduguri

Wata sanarwa da Birgediya Janar Sani K. Usman ya fitar a madadin hafsan hafsoshin sojan kasa Laftanal Tukur Burutai ta ce dakarun soji Najeriya 53 ne suka jikkata sakamakon harin.

An samu koma baya cikin yakin da sojin Najeriya keyi da 'yan Boko Haram cikin kwanakin nan bayan 'yan ta'addan suna ta kai hare-hare a sansanin sojin cikin makonni biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel