Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwar fara daukar aiki

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwar fara daukar aiki

A kokarin da ake yi na maganin matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya, rundunar 'yan sandan kasar ta sanar da cewa a yau Alhamis 29 ga watan Mayu ne za ta fara aiwatar da shirin daukar sabbin ma'aikata.

A cikin sanarwar da rundunar ta fitar shafinta na Twitter @PoliceNg ta nuna cewa shirin daukar dan sandan kyauta ne don haka ta nemi duk wanda ya cancanta kan ya gaggauta zuwa shafinta na yanan gizo www.policerecruitment.ng domin ya cike bayyanan da ake bukata.

Hukumar ta ce za a rufe shafin yanan gizon na daukan aikin makonni 6 daga yau.

DUBA WANNAN: Kotu ta daure shugaban hukumar UBEC, Murtala Adamu, shekaru 41 a gidan yari

Sanarwar da hukumar ta fitar ya bayyana cewa dukkan mai sha'awan shiga aikin ya kamata cika wasu ka'idoji kamar haka:

1. Ya kasance dan kasa ne kuma ya mallaki lambar dan kasa wato NIN

2. Shekarunsa ba su gaza 18 - 25 ba.

3. Ana bukatar shaidan karatu a kalla na kammala sakandire tare da samun credit a kalla 5 ciki har da turanci da lissafi

4. Ya kasance mutum mai hali na nagari

5. Idan na miji ne tsawonsa kar ya gaza 1.67m idan kuma mace ce kar ta gaza 1.64

6. Fadin kirjinsa kada ta gaza 86cm ko (34 inches)

7. Ya kasance ba shi da wata nakasa da za ta iya hana shi/ta gudanar da ayyukan da ake bukata daga dan sanda

8. Mutum ya kasance baya dauke da juna biyu a lokacin daukan aikin

9. Ya kasance ba shi da wata bashi da ta masa katutu

10. Duk mai neman shiga aikin dan sandan kuma zai nemi guaranto wanda zai saka masa hannu misali hakimai, alkalan kotun majistare, shugabanin kananan hukumomi, shugabanin makarantu, ma'aikatan gwamnati wadda sun wuce matsayi na 12, dan sanda wanda bai gaza matsayin CSP ba ko Soja wanda bai gaza mukamin Laftanant kwanel ba.

Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta fara daukan sabbin 'yan sanda

Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta fara daukan sabbin 'yan sanda
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel