Harin Metele: Rayukan Dakaru 23 sun salwanta, 31 sun jikkata - Hukumar Sojin Kasa

Harin Metele: Rayukan Dakaru 23 sun salwanta, 31 sun jikkata - Hukumar Sojin Kasa

Hukumar sojin kasa ta Najeriya ta yi karin haske tare da bayar da tabbaci kan adadin rayukan dakarun soji da suka salwanta a sanadiyar harin mayakan Boko Haram da ya auku cikin kauyen Metele na jihar Borno makonni biyu da suka gabata.

Yayin bayar da tabbacin ta hukumar sojin ta bayyana cewa, rayukan dakaru 23 ne kacal suka salwanta yayin da 31 suka jikkata a sakamakon harin mayakan Boko Haram na ranar 18 ga watan Nuwamba da ya auku a garin Metele da ke Arewacin jihar Borno.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, wannan adadi ya sabawa rahotanni na adadin kimanin dakaru 44 zuwa 100 da ake zargin sun rasa rayukan su yayin aukuwar harin da ya dimauta al'ummar kasar nan.

Shugaba Buhari yayin ziyarar Dakaru jiya a jijar Borno
Shugaba Buhari yayin ziyarar Dakaru jiya a jijar Borno
Asali: Depositphotos

Majiyar Legit.ng ta samu wannan rahoto cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Sani Usman ya zayyana a jiya Laraba a madadin shugaban hafsin sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai.

Babban jami'in ya bayyana cewa, ko shakka ba bu mayakan Boko Haram sun zartar da hare-hare kan dakaru a tsakanin ranar 2 zuwa 18 ga watan Nuwamba cikin sansanansu da ke Kukawa, Ngoshe, Kareto da kuma Gajiram.

KARANTA KUMA: Alhazai 5 na Jihar Zamfara sun rasa rayukansu a Kasa mai Tsarki

Birgediya Janar Usman ya ke cewa, a sanadiyar aukuwar wannan munanan hare-hare ya sanya dakaru 16 suka sadaukar da rayukansu yayin da 12 suka jikkata a faggen fama.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shilla jihar Borno inda ya jajantawa dakaru tare da kara ma su karfin gwiwa da kuma tsayuwar daka ta gwamnatinsa wajen inganta harkokin su na gudanarwa da jin dadi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel