Fusatattu sun kashe jami’in SARS din da ya harbe dan LASTMA

Fusatattu sun kashe jami’in SARS din da ya harbe dan LASTMA

Fusatattun mutane sun kashe jami’in SARS wanda ya harbe wani jami’in kula da zirga-zirgan motoci na jihar Lagas wato Lagos State Traffic Management Authority (LASTMA), Adeyemo Rotimi, a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba, inji wani jami’i.

Legitng ta ruwaito yadda aka kashe Mista Rotimi da misalin karfe 6 na yammacin ranar Laraba, yayinda ya tsayar da wani dan sandan SARS a lokacin wani cunkoso a titi.

Da suke Magana kan mumunan lamarin, hukumar LASMA ta tabatar da lamarin mutuwar jami’in nata a shafinta na twitter a ranar Alhamis, 29 ga watan Nuwamba.

Fusatattu sun kashe jami’in SARS din da ya harbe dan LASTMA

Fusatattu sun kashe jami’in SARS din da ya harbe dan LASTMA
Source: Depositphotos

Daga bisani sai kuma jami’in hukda da jama’a na hukumar, Yomi Shogunle ya je shafinsa na twitter inda ya sanar da cewa fusatattu sun farma jami’in SARS din da ya kashe jami’inta inda ya mutu shima yayinda ake gaggawan kai shi asibiti.

KU KARANTA KUMA: Fusatattun mutane a Kano sun yi wa ma’aikatan KEDCO dukan tsiya

Yayinda Mista Shogunle bai bayyana sunan jami’in a, kakakin yan sandan jihar Lagas, Chike Oti, a wata sanarwa ya bayyana shi a matsayin Olukunle Olonode.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel