Boko Haram na kai wa sojoji farmaki da jirage marasa matuka

Boko Haram na kai wa sojoji farmaki da jirage marasa matuka

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa yan ta’addan Boko Haram sun fara amfani da jirage marasa matuka wajen kai farmaki a kan cibiyoyin tsaro na sojojin kasar.

Hukumar sojin ta ce ta kula cewa wasu mahara daga kasashen waje na shiga Najeriya domin taimakawa kungiyar yan ta’addan a hare-hare da take kai wa jami’an tsaron kasar.

A cewar wata sanarwa daga hannun Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, shugaban hafsan sojojin kasar, Laftanal Tukur Burutai ya ce yan ta'addan sun fara amfani da jiragen ne da kuma mayakan waje cikin watanni biyu zuwa uku da suka gabata.

Boko Haram na kai wa sojoji farmaki da jirage marasa matuka

Boko Haram na kai wa sojoji farmaki da jirage marasa matuka
Source: UGC

Sanarwar ta kuma bayyana ainahin adadin jami'an da suka rasa ransu a harin Matele cewa sojoji 23 aka kashe a harin a ranar 18 ga watan nan na Nuwamba, sannan wasu 31 kuma suka jikkata.

KU KARANTA KUMA: 2019: Dan majalisar wakilai na APC ya sauya sheka zuwa SDP

A baya mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a matsayinsa na shugaban kasa da kuma karfin da yake da shi, zai tabbatar da cewa gwamnati ta samar da makaman yakin zamani domin kawar da haukan Boko Haram.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a birnin Maiduguri, jihar Borno a yau Laraba, 28 ga watan Nuwamba yayinda ya tafi halartan taron babban hafsan sojin Najeriya da ke gudana a jihar.

Ya jajantawa hukumar sojin Najeriya bisa ga rashin akalla sojoji 44 da sukayi a makon da ya gabata sakamakon harin Boko Haram kan barikin Matele dake arewacin jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel