Abun bakin ciki yayinda jami’in SARS ya harbe jami’in LASTMA har lahira

Abun bakin ciki yayinda jami’in SARS ya harbe jami’in LASTMA har lahira

Wani da ake zargin jami’in ya sanda masu yaki da yan ta’adda ne (SARS) ya hari wani jami’in kula da cunkoso a titi na jihar Lagas wato State Traffic Management Authority (LASTMA) har lahira.

A cewar jaridar The Nation, lamarin ya afku ne a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba a shataletalen Iana-Ipaja da misalin karfe 6 na yamma.

Jami’in LASTMA din ya tsayar da shi kan lamarin zirga-zirgan motoci.

Legit.ng ta tattaro cewa sai jami’in ya sauka sannan ya gargadi jami’in da ke kula zirga-zirgn motocin kan cewa kada ya sake tayar da shi, inda ya kara da cewa bashi da yancin yin haka.

Abun bakin ciki yayinda jami’in SARS ya harbe jami’in LASTMA har lahira

Abun bakin ciki yayinda jami’in SARS ya harbe jami’in LASTMA har lahira
Source: UGC

A yayinda suke musayar zafafan kalamu, sai ami’in ya fusata ya koma motarsa, inda ya fito da bindiga sannan ya harbi dan LASTMA din. Mutane da dama sun gudu don neman tsira bayan sun ji karar bindiga.

An tattaro cewa an kama jami’in wanda ba’a bayyana sunansa ba tukuna.

Idanun shaida sun ce jami’in na tuka motar Sport Utility Vehicle (SUV) ne.

KU KARANTA KUMA: 2019: Dan majalisar wakilai na APC ya sauya sheka zuwa SDP

An kai jami’in da ya mutu asiitin Ifako-jaye inda anan aka tabbatar da mutuwar nasa.

An mika gawarsa zuwa dakin ajiye gawa na Yaba, da ke Lagas. Kakakin hukumar LASTMA, Mahmud Hassan ya tabbatar da lamarin.

Hassan ya ce ana nan ana gudanar da bincike domin gano jami’an biyu da lamarin ya faru a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel