Majalisar dattawa ta amince da makarantun jami’a a mahaifar shugaban kasa, da wasu 9

Majalisar dattawa ta amince da makarantun jami’a a mahaifar shugaban kasa, da wasu 9

Majalisar dattawa a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwama ta amince da samar da sabbin makarantun gaba da sakandare 10 a fadin kasar.

An yanke shawarar ne bayan yan majalisar dokoki sun samu rahoton kwamitin majalisar dattawa kan makarantun gaba da sakandare da TETFund, wanda shugaban kwamitin, Jibrin Barau ya gabatar domin a duba.

Manyan makaratun gaba da sakandare da majalisar dattawa ta amince da su harda wani makarantar polu da za’a yi a mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu uhari, Saura a jihar Katsina.

Yan majalisa sun amince da cewa za’a bude makarantun ne domin cike guraben ilimi a kasar.

Majalisar dattawa ta amince da makarantun jami’a a mahaifar shugaban kasa, da wasu 9
Majalisar dattawa ta amince da makarantun jami’a a mahaifar shugaban kasa, da wasu 9
Asali: Twitter

Sun kuma nuna yakinin cewa wannan mataki zai taimaka wajen yakar jahilci a kasar.

Majalisar ta kuma bayyana cewa amince wa kafa makarantun yayi daidai da manufar samar da makarantun poli a jihohi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Makarantun da aka amince ma wa sune; Federal Polytechnic, Kabo; Federal Polytechnic Daura; Federal University of Education, Aguleri; National Institute of Construction Technology and Management and Federal Polytechnic, Ikom.

Sauarana sune kwalejin kimiyya na Arochukwu, jihar Abia; Federal Polytechnic Langtang, jihar Plateau; Federal College of Education, Usugbenu-Irua; Federal University of Technology, Manchok da kuma Federal Polytechnic Kwale, jihar Delta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel