Fusatattun matasa sun yi wa jami’an NEPA dukan tsiya

Fusatattun matasa sun yi wa jami’an NEPA dukan tsiya

Fusatattun mazauna yankin Sharada Malam a garin Kano sun kai wa tawagar yanke wuta da karban kudaden shiga na hukumar Kano Electricity Distribution Company (KEDCO) hari.

Kakakin KEDCO, Mohammed Kandi ne ya bayyana hakan, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa Kandi ya bayyana cewa biyu daga cikin tawagar Ali Mohammed da Abdulkadir Waziri, sun ji rauni a lokacin harin.

Fusatattun mutane a Kano sun yi wa ma’aikatan KEDCO dukan tsiya
Fusatattun mutane a Kano sun yi wa ma’aikatan KEDCO dukan tsiya
Asali: UGC

Mohammed Isah, jagoran tawagar ya kuma bayyana cewa mutanen sun yi wa macen cikinsu barazana.

KU KARATA KUMA: 2019: Jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Ya bayyana cewa maharani sun yi yunkurin yiwa macen zigidir, amma wasu bayin Allah sukr cece su.

A cewarsu suna ba mutanen yankin sharada wuta na tsawon sa’o’i 20 amma duk lokacin da suka je karban kudi ko yanke wutan wadanda basu biya ba sai su far masu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel