Gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun kasafta naira biliyan 788 a watan Oktoba

Gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun kasafta naira biliyan 788 a watan Oktoba

Gwamnatin tarayya, na jihohi da na kananan hukumomi sun raba kimanin naira biliyan dari bakwai da tamanin da takwas da miliyan goma sha uku (N788,013,000,000) daga baitil malin kasa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin ofishin babban akanta na kasa,Oise Johnson ne ya bayyana haka a ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, inda yace an gudanar da taron kasafta kudin ne a jahar Kaduna, inda yace an samu karin naira biliyan 89.42 daga kudin watan Satumba.

KU KARANTA; Bahallatsar naira biliyan 9: Gwamna El-Rufai ya maka jami’ar ABU da KadPoly gaban kotu

“Hukumar kasafta kudaden gwamnati ta bayyana cewar an kudi naira biliyan 682.16, wanda ya dara naira biliyan 569 da aka samu a watan Satumba da bambamcin naira biliyan 112.88.

“Haka zalika an samu karin sayar da gangan main a Najeriya da kusan ganga dubu dari takwas da ashirin, wanda hakan ya kara adadin kudin da aka samu zuwa dala miliyan hamsin da hudu fa dubu dari da casa’in, $54.19. sai dai farashin gangar mai ya fadi daga dala 75.69 zuwa dala 73.92.

“Don haka jimillan kudaden shiga da aka samu shine naira biliyan 682.16, amma gaba daya kudin da aka raba na watan Oktoba shine naira biliyan 788.13, idan aka hada da kudaden amfanin kaya VAT.” Inji shi.

Daga karshe yace gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 284.3, gwamnatocin jihohi sun samu naira biliyan 144.2, kananan hukumomi sun samu naira biiyan 111.2, jihohin dake samar da arzikin man fetir sun samu naira biliyan 58.09.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai babban akanta na kasa, kwamishinonin kudi na kafatanin jihohin Najeriya, ma’aikatan hukumar tattara haraji ta kasa FIRS, manyan akantocin jihohin Najeriya 36, jami’an ofishin kasafin kudi na gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel