Gwamnati na ta taka rawar gani ta dakusar da ta'addanci Boko Haram a jihar Borno - Buhari

Gwamnati na ta taka rawar gani ta dakusar da ta'addanci Boko Haram a jihar Borno - Buhari

- Gwamnati na ce ta taka rawar gani wajen dakusar da ta'addanci Boko Haram a jihar Borno inji Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya ziyarci fadar Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi

- Tsayuwar daka ta gwamnatin Buhari ta dakusar da kaifin kungiyar ta'adda ta Boko Haram

A jiya Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta taka muhimmiyar rawar gani wajen dakusar da tsanani na ta'addancin Boko Haram a jihar Borno wanda da tuni wani labari ake ji ba wannan ba.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito shugaba Buhari ya bayyana cewa, da ba don jajircewa da tsayuwar daka ta gwamnatinsa akan tsageranci na kungiyar ta'adda ta Boko Haram a jihar Borno, tuni da halin da al'ummar jihar za su tsinci kansu ya yiwa na yanzu fintinkau.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a fadar mai Martaba Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi, yayin ziyarar aiki ta sauke nauyin al'ummar kasar nan da ya rataya kane-kane a wuyansa.

Fadar shugaban kasa cikin wannan mako ta bayar da sanarwa cewa shugaba Buhari ya soke tafiyarsa ta zuwa garin Daura domin samun dama ta kai ziyara jihar Borno wajen ziyarar jaje sakamakon aukuwar wani mummunan hari na mayakan Boko Haram da ya salwantar da rayukan dakarun soji da dama.

Gwamnati na ta taka rawar gani ta dakusar da ta'addanci Boko Haram a jihar Borno - Buhari
Gwamnati na ta taka rawar gani ta dakusar da ta'addanci Boko Haram a jihar Borno - Buhari
Asali: Depositphotos

Harin ya auku ne a tsakanin ranar 2 zuwa 18 ga watan Nuwamba inda dakarun soji da dama suka sadaukar da rayukan su a filin daga yayin fafatawa da 'yan ta'adda wajen kare martaba ta kasar su kamar yadda hukumar sojin kasa ta bayyana.

KARANTA KUMA: Harin Metele: Rayukan Dakaru 23 sun salwanta, 31 sun jikkata - Hukumar Sojin Kasa

Sai dai ko shakka ba bu wannan hari na daya daga cikin mafi munanan hare-hare da suka auku a kan dakarun sojin kasar nan a bisa mahanga ta jaridar Legit.ng

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, tsohon kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Kukasheka, ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun fara amfani da jiragen sama marasa matuka wajen zartar da hare-hare kan sasanan dakarun kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel