Kungiyoyin Musulmai sun nemi a nada Inyamiri babban limamin Masallacin Abuja

Kungiyoyin Musulmai sun nemi a nada Inyamiri babban limamin Masallacin Abuja

Musulman kabilar Ibo sun bayyana damuwarsu kan yadda mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ke jan kafa kan batun nada wani daga cikinsu, watau Inyamiri a matsayin babban limamin Masallacin Abuja.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Inyamurai Musulmai sun bayyana haka ne ta wata kungiyasu, IMF, inda shugabanta, Suleiman Afikpo da Dakta Muhammad Amaechi suka bayyana cewa sun dauki alkawarin da Sultan yayi musu da muhimmanci, amma har yanzu ba’a cika ba.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun kasafta naira biliyan 788 a watan Oktoba

A yanzu haka sun bayyana cewa wannan alkawari na shan kwakwazo daga sauran musulmai yan kabilar ibo, inda wasu ke ganin tamkar an mayar dasu saniyar warene saboda basu fito daga Arewacin Najeriya ba.

“Wa ya takura ma Sultan ya furta wannan magana, ko kuwa dama ba da gaske yake bane? Bayan kuwa a lokacin da yayi wannan magana a ranar 9 ga watan Oktoba dukkanin jaridun kasarnan sai da suka bugashi.

“Sakamakon wannan alkawari da Sultan yayi yasa muka shirya wani muhimmin taro, inda muka gayyaci Malamai daga cikinmu, sa’annan muka tantancesu, muka ware mutane uku daga cikinsu wadanda muka aika sunayensu ga mai alfarma sarkin Musulmi.

“Amma abin takaici har yanzu babu wani martani daga fadar, kuma babu wanda ya cike gurbin limancin, don haka muna jin zafin wannan mataki, kuma muna yi ma mahukunta tuni da su duba kukanmu da idon tausayi.” Inji kungiyar.

Haka zalika kungiyar ta ja hankalin mahukunta ga gurbin da mukamin daraktan mulki a hukumar koli ta musulmai ta kasa, NSCIA, inda tace har yanzu ba’a nada kowa ba, bugu da kari kujerar darakta mai kula da kudu masu gabashin kasarnan a hukumar alhazai a bude take tun bayan karewar wa’adin mulkin Saleh Okenwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel