Latest
Akalla rayukan kananan yara uku ne suka salwanta a sanadiyar tsumangiyar kan hanya da kuma matsanancin karancin abinci mai gina jiki a karamar hukumar Mani ta jihar Katsina da ta kasance mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hukumar da ke kula da hanyoyi na jihar Niger (NIGROMA), ta soma aikin gyaran wasu bangarori na hanyar Minna zuwa Bida da suka lalace. Gwamnatin jihar ta bukaci matafiya da su kara hakuri yayinda take kokarin gyara hanyar.
Kimanin sa'o'i 24 bayan harin da yan bindiga suka kai jihar Taraba inda suka kashe mutane biyu, wasu yan barandan sun hallaka wani limanin Katolika, Rabaren David Tanko, a Kufai Amadu, karamar hukumar Takum ta jihar.
Daya daga cikin yara mafi kwazo a duniya Joshua Beckford na shirin kawo ziyara Najeriya. An bayyana Beckford a matsayin daya daga cikin yara mafi azaka a duniya yayinda ya kammala karatu daga jami’ar Oxford yana da shekara 14.
Duk wanda yake bibiyar abubuwan da suka shafi masana'antar Kannywood ya san cewa an sha wata badakala a 'yan kwanakin nan da suka wuce. Badakalar da aka sha din kuwa ita ce maganar kama wani babban mai bada umarni a cikin fina...
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta kama wasu manyan jami'an kamfanin wutar lantarki na Neja Delta Power Holding Company (NDPHC), akan dala biliyan sha shida da tayi batan dabo ta gyaran wutar lantarki a lokacin...
Abdullah Mohammed dan gidan gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed (Kauran Bauchi), ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram inda yake nuna jikin wata mota da ya siya kirar Rolls Royce, mai dan karen tsada...
Tun farkon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba a bai wa kabilar Nupe mukami ko guda daya ba, misalin minista ko shugaban wata babbar ma'aikata. Kabilar Nupe dai sune kabila ta biyar da suka fi yawa a fadin Najeriya a yadda..
Hukumar yan sandan jihar Katsina ta alanta cewa an ceto mata 10 cikin 15 da akayi garkuwa da su a ranar Talata, 27 ga Agusta a kauyen Wurna, karamar hukumar Wurna jihar jihar.
Masu zafi
Samu kari