Joshua Beckford: Yaron da ya shiga jami’a yana da shekara 6 na shirin ziyartar Najeriya, zai gina makaranta a Kaduna

Joshua Beckford: Yaron da ya shiga jami’a yana da shekara 6 na shirin ziyartar Najeriya, zai gina makaranta a Kaduna

Daya daga cikin yara mafi kwazo a duniya Joshua Beckford na shirin kawo ziyara Najeriya. An bayyana Beckford a matsayin daya daga cikin yara mafi azaka a duniya yayinda ya kammala karatu daga jami’ar Oxford yana da shekara 14 a duniya.

Ana sanya ran dan baiwan zai ziyarci Najeriya inda zai tara kudi don gina wata makaranta a jihar Kaduna.

Shugabar hukumar yan Najeriya a kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, na daga cikin yan Najeriyan da suka wallafa batun zuwa Beckford Najeriya a shafin twitter.

Duk da kalubalen da ya fuskanta na rashin lafiya da ya hana shi hulda da jama’a, an tattaro cewa Beckford ya fara sanin abubuwa da wuri.

"Wannan shine Joshua, wanda ya kasance yaro mafi karancin shekaru da yayi karatu a jami'ar Oxford yana da shekara 6 sannan ya kammala karatu a lokacin yana da shekara 14 a duniyya daga sashin tarihi da ilimin yanayin halitta. Zai kasance a jihar Lagas domin tara kudin aikin gina makarantarsa a Kaduna. Ana daukarsa a matsayin daya daga cikin mutane mafi kwazo a duniya."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kwashe sojojin da ke da hannu a kisan Taraba zuwa hedkwatar soji da ke Yola

A lokacin da yake da watanni 10 a duniya ya iya karatu, rubutu, da kuma fahimtar harafen baki. Da ya cika shekara biyu, ya iya karatu sosai sannan a lokacin da yake da shekara uku, Beckford ya iya yaren kasar Japan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel