A karshe gwamnatin Niger ta fara aikin gyaran hanyar Minna zuwa Bida

A karshe gwamnatin Niger ta fara aikin gyaran hanyar Minna zuwa Bida

Hukumar da ke kula da hanyoyi na jihar Niger (NIGROMA), ta soma aikin gyaran wasu bangarori na hanyar Minna zuwa Bida da suka lalace.

Misis Mary Barje, babbar sakatariyar labarai na Gwamna Abubakar Bello a wani jabin da ta saki Minna, babbar irnin jihar a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta, ta jaddada shirin gwamnatin jihar na sake shimfida hanyar da kuma mayar da hanyar Minna zuwa Bida guda biyu.

Bello ya bayyana cewa hanyar wacce aka gina ta shekaru 35 da suka gabata, ta gama lokacinta kuma tana bukatar cikakken kulawa.

Gwamnan ya sha alwashin cewa za a sake gina hayar ne bayan ruwan sama ya dauke.

Ya bukaci matafiya da su yi hakuri da gwamnatin yayin da take iya kokarinta don ganin an rage wahalar da matafiya ke fuskanta.

NAN ta rahoto cewa hanyar mai tsawon kilomita 83 ta yanke a ranar Talata bayan ruwan sama da aka cigaba da yi har na tsawon kwana uku, wanda hakan ya sanya matafiya cikin mawuyacin hali. An dakile hanyan saboda rushewar babban gada.

Wadanda lamarin ya fi shafa sun hada da matafiya masu zuwa da dawowa daga yankin Kudu maso yammacin kasar.

NAN har ila yau ta rahoto cewa gwamnatin jihar tace zata kashe naira biliyan 1.55 wajen aikin gyaran hanyan.

KU KARANTA KUMA: Joshua Beckford: Yaron da ya shiga jami’a yana da shekara 6 na shirin ziyartar Najeriya, zai gina makaranta a Kaduna

Za ayi gyaran hanyan ne a sashe biyu, sashe na farko zai kama daga Garatu zuwa Minna, wanda zai ci naira miliyan 800 sannan sashe na biyu zai kama daga Garatu zuwa Bida, wanda zai kama naira miliyan 750.

Ya bayana cewa akwai akalla wurare 11 marasa kyau a hanyar Bida-Minna wadanda ke iya saka rayukan matafiya cikin hatsari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel