Yadda gwamnan Bauchi ya sha zagi a wajen mutane bayan danshi ya sanya hoton wata dankareriyar mota da ya siya ta miliyoyin nairori

Yadda gwamnan Bauchi ya sha zagi a wajen mutane bayan danshi ya sanya hoton wata dankareriyar mota da ya siya ta miliyoyin nairori

- Mutane sun yiwa gwamnan jihar Bauchi kaca-kaca a kafar sadarwa ta yanar gizo

- Hakan ya biyo bayan wani hoto da dan sa ya sanya na wata dankareriyar mota da ya siya ta miliyoyin nairori

- Bayan motar dan nashi mai suna Abdullah ya kuma sanya hoton wani agogo mai dan karen kyau

Abdullah Mohammed dan gidan gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed (Kauran Bauchi), ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram inda yake nuna jikin wata mota da ya siya kirar Rolls Royce, mai dan karen tsada.

Bayan motar da dan gidan gwamnan ya nuna ya kuma nuna hoton wani agogo dake hannunsa wanda shima alamu suka nuna ba irin na yaku bayi bane.

Wannan hotuna da dan gidan gwamnan ya sanya sun jawo kace-nace matuka a shafukan sada zumunta, inda wasu suka dinga yin Allah wadai da irin wannan gwamnati da babu abinda suke yi sai azurta kansu da 'ya'yansu.

KU KARANTA: Dan Allah nan gaba indai za aje yiwa wani dan siyasar Najeriya duka a kirani zan bayar da gudummawa - Dan gidan Fela Kuti

Wani da ya boye sunan shi cewa yayi: "Yanzu hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, da kuma hukumar 'yan sanda duka baza su ga wannan ba ballantana su bincike shi."

Shi kuma wani mai suna Kinging cewa yayi: "Mai yasa talakawa suka tsani masu kudi ne? Wannan mutanen dama can masu arziki ne tun kafin su hau mulki. Kuje kuyi bincike akan ahalinsu zaku fahimci me nake fada muku."

Haka shi kuma wani da ya sanya sunansa da Lyrics Love cewa yayi: "Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ku kama duka da da uban, basu da banbanci da 'yan damfara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel