Yanzu-yanzu: An kashe babban malami addini, an bankawa gawarsa wuta a Taraba

Yanzu-yanzu: An kashe babban malami addini, an bankawa gawarsa wuta a Taraba

Kimanin sa'o'i 24 bayan harin da yan bindiga suka kai jihar Taraba inda suka kashe mutane biyu, wasu yan barandan sun hallaka wani limanin Katolika, Rabaren David Tanko, a Kufai Amadu, karamar hukumar Takum ta jihar.

Limamin wanda yake hanyar tafiyarsa zuwa Takum domin zaman sulhu da wasu abokansa kan yadda za'a shawo kan rikicin da yaki ci yaki cinyewa tsakanin yan kabilar Jukun da Tibi, ya gamu da ajalinsa.

Tabbatar da hakan ga manema labarai, shugaban kwamitin, Shiban Tikari, ya bayyana cewa bayan sun kashehi, sai suka bankawa motarsa da gawarsa wuta.

Tikari ya kara da cewa Rabaren David Tanko dan karamar hukumar Wukari ne kuma ana zargin yan kabilar Tibi da kai wannan hari.

KU KARANTA: El-Zakzaky da matarsa zasu sake komawa kasar waje neman lafiya

Hakazalika ya daura laifin dukkan asaran rayuka da dukiyan da ya addabi kudancin Taraba kan yan kabilar Tibi, ya ce har yanzu babu wanda ya san dalilin da yasa suke haka.

Dukkan kokarin da majiyarmu tayi na jin matsayar hukumar yan sanda bai cimma nasara ba. Kakakin yan sandan jihar, David Misal, ya ki daukan wayarsa.

Jihar Taraba tana fusktantar kalubalen rashin tsaro musamman a karamar hukumar Wukari tsakanin yan kabilar Jukun da Tibi.

A ranar Laraba, an kashe wani dalibin makarantar ECWA cikin gonarsa a karamar hukumar Donga na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel