Tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta kafa babban sansani a jihar Niger

Tsaro: Rundunar sojin Najeriya ta kafa babban sansani a jihar Niger

Rundunar sojin Najeriya ta kafa wani babban sansani a Kotonkoro da ke karamar hukumar Mariga na jihar Niger domin magance matsalar garkuwa da mutane, fashin shanu da kuma ayyukan yan bindiga a yankin.

Birgediya Janar Gideon Ajetonmobi, kwamandan, Brigade 31, Minna, ya bayyana hakan yayinda yake kewayawa da babban sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ahmed Matane, ilahirin sansanin, a wani ziyarar ban girma.

A cewar wani jawabi daga jami’in labaran sakateren gwamnatin, Lawal Tanko, a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta, kwamandan brigade din yace an kafa wannan sansani ne domin magance rashin tsaro da ya addabi yankin da wasu yankunan jihar.

Ya bayyana cewa akwai bukatar kafa sansanin sojin tunda jihar na raba iyaka guda da Zamara da kuma Kebbi.

A cewarsa, sansanin zai kawo mafitar da ake bukata akan zirga-zirgan yan bindiga, masu garkuwa da mutane da barayin shanu daga jihohin da ke makwabtaka da Niger.

Ajetonmobi ya fada ma sakataren gwamnatin jihar cewa sansanin wanda aka kafa shi akan fili mai girman mita 700 bisa 700, tare da kimanin sojoji 200 sun shirya tunkarar duk wasu yan ta’adda.

KU KARANTA KUMA: Aiki ga mai kareka: Babban Sufetan Yansanda ya tura Abba Kyari hanyar Kaduna-Abuja

Da yake jawabi ga jami’an sansanin, Matane ya yaba ma rundunar sojin Najeriya akan kafa sansanin da suka yi, sannan cewa kasancewar sojin a yankin zai kawo karshen fashi da makami, sace-sacen mutane da fashin shanu.

Ya ba sojojin da ke sansanin tabbacin cewa a shirye gwamnatin take ta basu karin kayayyaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel