Bidiyo: Masu garkuwa da mutane sun cafke Jaruma Maryam KK, amma daga bisani tasha dakyar

Bidiyo: Masu garkuwa da mutane sun cafke Jaruma Maryam KK, amma daga bisani tasha dakyar

- Wasu masu garkuwa da mutane sun sace jarumar masana'antar Kannywood dinnan mai suna Maryam KK

- Sai dai kuma an bayyana cewa sun sako ta daga baya, inda aka dauko ta gaba daya ta jigata ta kuma wahala

- An bayyana cewa tun daga lokacin da aka dauko ta har lokacin da suka iso gida bata bude baki tayi magana ba

Wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta ya bayyana yadda miyagun masu garkuwa da mutane suka sace sabuwar jarumar fina-finan Hausa ta masana'antar Kannywood, Maryam KK.

A bidiyon dai an nuno yadda jarumar ta jigata inda take ta faman rusa kuka, jikinta kuma duk ya kuce, sai dai saboda ba a bayar da wani bayani ba sosai, har yanzu bamu da masaniya akan inda aka sace ta da kuma yadda aka yi aka samo ta.

Amma dai a cikin bidiyon mun jiyo muryar wata mata da take yin waya tana magana akan irin halin da jarumar ta shiga, ta bayyana cewa tun lokacin da suka daukota ta kasa cewa uffan in banda uban kuka da take rusawa.

KU KARANTA: ICPC: Mun ceto mata 14 da aka yi garkuwa dasu a gidan wani ma'aikaci wanda ke da hannu a badakalar kudade a kasar nan

An nuno 'yan uwa da abokan arziki da suka je domin taya ta jaje da wannan lamari da ya sameta, inda da yawa daga cikinsu suma kukan suke ta faman yi don tausayi na irin halin da take ciki.

Idan ba a manta ba a jiya ne wasu masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da kusan mutane bakwai akan babban titin Kaduna zuwa Abuja, inda aka bayyana cewa a cikin mutanen da suka sace din hadda daliban jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria guda uku.

Amma a karshe dai an bayyana cewa jami'an hukumar 'yan sanda sun samu nasarar kwato daliban jami'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel