Karancin abinci mai gina jiki ya kashe yara 3 a Katsina

Karancin abinci mai gina jiki ya kashe yara 3 a Katsina

Akalla rayukan kananan yara uku ne suka salwanta a sanadiyar tsumangiyar kan hanya da kuma matsanancin karancin abinci mai gina jiki a karamar hukumar Mani ta jihar Katsina da ta kasance mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Babu shakka karancin abincin mai gina jiki musiba ce da ke murkushe dukkanin wani bil Adama da ta kama matukar ba a dauki matakin magance ta ba cikin gaggawa.

Wata majiyar rahoto kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito ta bayyana cewa, kananan yara uku da suka hadar da mace daya da kuma maza biyu sun yi kacibus da ajali a ranar Alhamis da Juma'ar da ta gabata.

Majiyar ta bayyana cewa, kananan yaran uku sun ce ga garin ku nan a sanadiyar matsancin karancin abinci mai gina jiki da ya kwakware masu dukkanin wata garkuwa ta lafiyar jiki.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, kananan yara uku sun riga mu gidan gaskiya a wata karamar cibiyar lafiya da ke karamar hukumar Manin jihar Katsina.

KARANTA KUMA: Farashin Biza: Gwamnatin Najeriya ta yi wa 'yan Amurka rahusa

A wani rahoton mai nasaba da wannan da muka kalato daga jaridar BBC Hausa, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, yara dubu dari hudu ne a yankin Kasai na Kasar Jamhuriyyar Congo ke fama da matsanancin karancin abinci mai gina jiki.

Hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da Asusun kula da kananan yara na majalisar wato UNICEF ya fitar, inda ya ce yaran na matukar bukatar agajin gaggawa domin kawo masu dauki na ceton rayukansu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel