Farawa da Bismillah: EFCC ta kama manyan yaran Obasanjo guda hudu kan $16b da suka cinye ta wutar lantarki

Farawa da Bismillah: EFCC ta kama manyan yaran Obasanjo guda hudu kan $16b da suka cinye ta wutar lantarki

- Hukumar EFCC ta kama manyan yaran Obasanjo da suka yi sama da fadi da wani bangaren na kudin gyaran wutar lantarki a shekarun baya

- Kama mutanen da aka yi yana nuni da irin kokarin da gwamnati ke yi na hukunta wadanda keda hannu a cikin wannan badakala

- Rahotanni sun nuna cewa da yawa daga cikin wadanda hukumar ke nema sun gudu zuwa kasashen ketare domin gujewa hukumar

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta kama wasu manyan jami'an kamfanin wutar lantarki na Neja Delta Power Holding Company (NDPHC), akan dala biliyan sha shida da tayi batan dabo ta gyaran wutar lantarki a lokacin Obasanjo.

Mutane biyun suna daga cikin mutane hudu da hukumar ta kama ranar Larabar nan. Kama su din da aka yi yana nuni da irin kokarin da gwamnati take yi na hukunta mutanen da ke da hannu a wannan badakala.

Jami'an da aka kama din na Neja Delta din sun hada da shugaban fannin kudi, Marvel Emefiele da kuma wani shugaba shima da yake a bangaren kudin mai suna Eze M.C. Odigbo. Ana tunanin zasu bayar da naira miliyan dari takwas da hamsin a matsayin toshiyar baki ga al'ummar yankin.

KU KARANTA: Yadda gwamnan Bauchi ya sha zagi a wajen mutane bayan danshi ya sanya hoton wata dankareriyar mota da ya siya ta miliyoyin nairori

Sauran mutanen dake hannun hukumar EFCC din sun hada da manajan darakta Pivot Engineering Mr. Richard Ayibiowu da kuma manajan darakta na Chris Ejik Nigeria Limited, Mr. Christian Wjik Imoka.

Yanzu haka dai jami'an suna cigaba da bincike domin cafke sauran mutane goma sha takwas, cikinsu kuwa hadda tsofaffin gwamnoni guda biyu, tsohon shugaban banki, da kuma tsohon shugaban kamfanin jirgin sama.

Haka kuma kimanin kamfanoni 15 ne hukumar take gabatar da bincike akan su. Akwai jita-jitar cewa tsananin tsoro yasa wasu daga cikin wadanda keda hannu a wannan badakala sun gudu kasar waje domin buya daga farautar da hukumar ke yi musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel