Yan sanda sun ceto mata 10 daga hannun yan bindiga a Katsina

Yan sanda sun ceto mata 10 daga hannun yan bindiga a Katsina

Hukumar yan sandan jihar Katsina ta alanta cewa an ceto mata 10 cikin 15 da akayi garkuwa da su a ranar Talata, 27 ga Agusta a kauyen Wurna, karamar hukumar Wurna jihar jihar.

Kakakin hukumar yan sandan, ASP Anas Gezawa, a ranar Laraba ya tabbatar da cewa yan bindigan sun kai hari Kurfi kuma sun yi awon gaba da mata 15 wanda ya hada da diyar maigarin Wurna da surukarsa.

Hakazalika yace sun yi awon gaba da dabbobin da har yanzu ba'a adadinsu ba.

KU KARANTA: Sabon salon yakin da muka fara zai tilasta yan Boko Haram mika wuya - Janar Khalifa

Anas Gezawa yace: "Yan bindiga sun far ma kauyen Wurma, karamar hukumar Kurfi kuma sun yi garkuwa da mata 15 wanda ya hada da diyar maigari da surukarsa."

"Ana cigaba da kokarin ceto sauran da kuma damke yan barandan,"

Wani Mazaunin garin ya bayyanawa Manema labarai cewa ‘yan bindigan sun shigo Kauyen da kimanin karfe 12:00 na dare inda su ka shiga buda wuta a kowane gida na tsawon akalla sa’a uku.

Wadannan Miyagu da su ka tasan ma Kauyen na Wurma sun yi awon gaba da Mata da kananan yara da-dama. Bayan nan kuma an nemi mutane fiye da 50 amma babu wanda ya ji duriyarsu.

Wannan Bawan Allah da ya zanta da ‘yan jarida ba tare da bayyana sunansa ba, ya bada tabbacin cewa an yi masu gaba da dabbobi irin shanu da tumaki da kaji da kuma sutura da kayan abinci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel