Mansurah Abdulazeez: Yar asalin Kano ta samar da maganin kansa daga shukokin Afrika

Mansurah Abdulazeez: Yar asalin Kano ta samar da maganin kansa daga shukokin Afrika

Mansurah Abdulazeez, wata masaniyar ilimin kwayoyin halitta a cibiyar fasahar binciken halitta, jami’ar Bayero, Kano, ta kafa wani babban tarihi inda ta gano makagin cutar kansa.

Masaniyar kwayoyin halittar tayi bayanin komai game da bincikenta a wata hira tare da jaridar The Guardian.

Ku sani cewa Mansurah ta kuma lashe wani gasar binciken Najeriya na kasa na $86,000 a watan Yuni jim kadan bayan ta samu wani matsayi a kasar Spain a watan Nuwamban 2018.

Da take Magana akan tushen kimiyarta, mai binciken tace ta mayar da hankali a kimiya sosai a lokacin da take tasowa, inda ta kara da cewa ta so zama likita, amma sai ta kare da karantar fannin gwaje-gwaje a digirinta na farko da tayi a jami’ar Ahmadu Bello.

Tace ta fadada sosai a aikinta, inda ta ambaci cewa ya mayar da hankali wajen gano maganin cutar kansa daga shukoin Najeriya kamar irinsu bishiyoyin abubuwa masu bauri.

Mansurah Abdulazeez: Yar asalin Kano ta samar da maganin kansa daga shukokin Afrika
Mansurah Abdulazeez: Yar asalin Kano ta samar da maganin kansa daga shukokin Afrika
Asali: UGC

Ta kara da cewa, bincikenta ya kuma yi nazari akan sunadaren da ke yakar kansa daga shukokin, inda ta kara da cewa babu “wani yanayi guda ga dukkanin shukokin”.

Da aka tambaye ta kan dalilin da yasa shukokin Afrika ked a muhimmanci a bincikenta, Mansurah ta bayyana cewa suna dauke da tarin sinadaren maganin kansa sannan cewa har yanzu ba a karantar da su a cibiyoyin kimiya.

Tace wadannan shukoki na dauke da sinaran yakar kansa kamar su sabara da masu gargajiya ke amani da su wajen warkar da cutar daji.

KU KARANTA KUMA: Joshua Beckford: Yaron da ya shiga jami’a yana da shekara 6 na shirin ziyartar Najeriya, zai gina makaranta a Kaduna

Mansurah ta shawarci matan Afrika masu tasowa da ke da ra’ayi a karatar kimiya da su dunga halartan tarurruka a gida da waje a fanninsu domin su samu dabaru, makamai da kuma damar shiga cikin wadanda ake daukar nauyinsu.

Ta kuma kara da cewa neman tallafin manyan abokan aikinsu, yan uwa da abokai, himma da jajircewa zai kai su wajen da suke mafarkin zuwa a kimiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel